MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

ZAUREN GIRKE GIRKE: YADDA AKE MIYAR KWAI

DAGA AUWAL M KURA

Abubuwan hadawa
Kwai
Tarugu
Albasa
Curry da thyme
Garin citta kadan
Koren tattasai
Koren wake
Karas
Butter
Knor chicken ko Maggi chicken (ya danganta da irin dandano ki)
Yadda ake hadawa
1. Da farko zaki fasa kwanki a ciki wani karamin kwano, sai ki yanka albasa a ciki, ki ajiye a gefe.
2. Ki wanke ki cire dattin bayan carrots naki, ki wanke su Koren wake ,albasa dasu tarugunki, sai ki yanka su dogo dogo, bayan kin gama dauko carrot naki da koren wake, ki sa masa ruwan zafi sosai (tafasashshe), sai ki sa baking powder Ko kanwa a ciki ki rufe shi nadan wani lokaci, sai ki cire shi cikin ruwan sannan ki sake wanke shi ki tsane shi, sannan ki ajiye a gefe.
3. Daura tukunyarki akan wuta ki sa butter kadan ki narka, sai ki kawo albasarki ki yanka a ciki ki soya sama sama.
4. Dauko yankakken tarugunki ki sa a ciki da su maggi , garin citta kadan, curry da thyme sai ki kawo ruwan zafi kadan sai ki juya ki rufe shi na dan wani lokaci.
5. Sai ki dauko kwanki (wanda ki ka fasa a kwano) ki zuba cikin tukunya ki dake kan wuta ki rufe ki barshi nadan wani lokaci.
6. ki rage wuta sai ki bude ki kawo su carrot, koren wake ki sa sai ki juya shi a hankali ki kara rufeshi nadan wani lokaci har sai ruwan ciki ya shanye, sai ki sauke
za ki iya ci da soyayyen dankalin turawa ko doya. A ci dadi lafiya

Danna nan idan kana neman BIDIYON HAUSA masu ilimantar wa da NIshadantarwa musamman na Zamantakewa tsaknin Ma'aurata:


Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa

Updated: 2018-04-21 — 5:04 pm

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme