MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

YANDA AKE HADA MASA

UWAR GIDA 

da farko dai za ki fara wanke farin shinkafan ki wanda kikafi sani da shinkafan tuwo sannan ki tsiyaye ruwan da kika wanke amma ki sani wankewa zakiyi kamar sau uku ya wadatar sai ki sami roba ko kwano da dai ze dauke yawan kullun in kin nuko. sai kisa a ciki ki kai nika in kuma kina da injin nika to sai ki nika shi amma karyayi ruwa sannan ya nuku sosai

bayan kin kammala nikan na ki sai ki samu yis kisa aciki. ki rufe shi na kamar awa daya dan yayi miki auki. kisani in kina so kiyi da surine to da wuri zaki fara ba sai kin tashi yi ba dan ze iya miki gaddama.

bayan yayi awa daya uwar gida sai ki bude. daman kin dora tandan ki yana kan wuta manki na gyada na gefe sai kiyi shirin suya

in kuma kina son tafi da gidan ka ne ma’ana masan da ba sai da miya ba zalla za a ci shi to kada ki rufe shi bayan kin sa yis sai ki tabbatar kin sa masa magi da gishiri dai dai gwargwado tare da yanka albasa da atarugu da kori kayan dai dandano yaji da kyau kuma a ukula kar ya zarce misali.

sai ki rufe bayan yayi awa daya sai ki bude ki fara suya kar kuma kibar tandan naki ba mai a jikin sa dan shi ke sa masa yayi baki

Danna nan idan kana neman BIDIYON HAUSA masu ilimantar wa da NIshadantarwa musamman na Zamantakewa tsaknin Ma'aurata:


Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa

Updated: 2017-02-21 — 11:54 am

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme