MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

Yadda zaki hada Farfesun Kifi

Farfesun Kifi

INGREDIENTS:
?Kifi wanda kike dashi (cat fish or tilapia)
?Garin yaji/taruguni nikakke, citta, Kanunfari, masoro, tafarnuwa, albasa, citta, thyme, curry, gishiri, maggi, nutmeg, cray fish, gimba, dama sauran dukkanin kayan kamshin ki.
?Water.

PROCEDURE: Farko dai zaki wanke kifin sosai, sai ki dauko tukunya da babu komai a ciki, ki zuba kifin, ki zuba gishiri maggi da albasa da tafarnuwa, ki bashi kamar 10mnt. Idan kin bude bayan minti 10 sai ki zuba garin yajin ki da su citta da sauran kayan kamshin duka da cray fish sai ki jujjuya ki barshi har sai kifin ya dahu. Kada ki bari ya dahu har ya fara farfashewa sannan kada ki cika ruwa.

Another method ?

Shi kuma wannan ruwan zaki fara zubawa a tukunya dai dai yanda zai ishi kifin ki, idan ya tausa sai ki sanya kayan kamshin ki, sannan ki zuba albasan ki, kisa maggi dasu gishirI, ki sa garin yajin ki ko tarugu wanda ya jajjagu sosai yanda ba za’a ga alamun kayan miya ba, bayan sun dan yi kamar 5mnt haka suna tausa sai ki dauko wankakken kifin ki juye a ciki, idan ya dahu sai ki sauke.

Note: Ba’a sawa pepper soup kayan miya, shiyasa ake amfani da garin yaji, zaki iya sawa a miki zallan yajin tarugu da babu komai a ciki, wanda zaki na amfani dashi a pepper soup. Ko ki siyo borkono a daka miki shi yayi laushi wanda ba ya’yan.

Sannan ba’a yawan juya kifi da har sai ya farfashe kafin ki gama. A hankali zaki na juya shi saboda kada su farfashe.

Sannan ba’a sanya mai, sai dai in mutum yaso.

Yana da kyau ki tanadi kayan kamshin ki wainda dana lissafo saboda ban rubuta abin da zaa ce ba’a samu a kasuwa ba, wainnan a saukake zaki ssme a saukake, idan kika aika kasuwa wurin yarbawa zasu hada miki, ko sissiyo ki daka da kanki.

Sannan zaki iya sa mishi ganye amma busashe.

Ina fatan mutum 5 da suka bukaci rubutu akan haka zasu gani.

Yar’uwar ku Sadeeya Lawal Abubakar.
Zauren Girke-Girke.

Danna nan idan kana neman BIDIYON HAUSA masu ilimantar wa da NIshadantarwa musamman na Zamantakewa tsaknin Ma'aurata:


Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa

Updated: 2016-10-27 — 9:11 am

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme