MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

YADDA ZA AYI DAFA DUKA MAI KWAKWA uwar gida

Barkanmu da warhaka uwargida tare da fatan ana lafiya. A yau na kawo muku yadda ake dafa dafaduka mai kwakwa. Kamar yadda a kullum nake gaya muku bai kamata a rika yawaita yin girki iri daya ba. Idan har maigida ya kasance mai yawan son cin shinkafa, to sai a rika canza masa salon girkin shinkafar. Walau shikafa da miya ko dafaduka da sauransu. A sha karatu lafiya.

Abubuwan da za a bukata

·Shinkafa
· Garin kanumfari
· Ruwan kwakwa
· Tumatir
· Man gyada
·Albasa
·Attaruhu
· Garin tafarnuwa
· Magi
· Tumatirin gwangwani

Hadi

A tafasa ruwa sannan a zuba a kan shinkafa sai a ajiye a gefe. A dauko attaruhu a jajjaga da tafarnuwa idan ba a samu ta gari ba. Sannan a dora man gyada kadan a kan wuta idan ya yi zafi sai a soya kayan miya tare da tumatirin gwangwanin nan sai a yi ta gaurayawa har sai sun soyu. Idan sun soyu, sai a zuba ruwan kwa-kwan a kai tare da ganyen bay da kori da magi zalla ga marasa son cin gishiri. Domin sirrin kowani girki magi ne. A jira ta tafasa. Bayan ta tafasa Sai a wanke wancan shikafar ta fita tas sannan a zuba a hadin ruwan kwa-kwan nan.
Domin samun gardin wannan girkin, za a iya tafasa kaza ko kifi sai a yi girkin da ruwan da ruwan kwa-kwa. Sannan bayan an soya su za a iya amfani da man wajen yin girkin.

Danna nan idan kana neman BIDIYON HAUSA masu ilimantar wa da NIshadantarwa musamman na Zamantakewa tsaknin Ma'aurata:


Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa

Updated: 2017-03-22 — 8:48 am

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme