MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

YA KIKE SARRAFA BREAD?

12295507_593277167506462_1553911155682412395_nBread dai yawanci mun sanshi ne wurin yin break fast dashi, to amma yawanci muna cin bread ne tuwon shi, bamu kayata sa, ta hanyar da mai gida da yayan gida zasu samu canji a yayin yin breakfast. Don haka zan dan yi bayanin kadan daga cikin yanda zaki sarrafa shi.
1. Zaki samu slice bread (breadi mai yanka yanka) sai ki samu butter ki shafe shi a jikin sa, daga nan sai ki dauko toaster (injin gasa breadi) sai ki sanya a ciki, idan ya gasu zai nuna miki alama, sai ku sha da shayi. Yana da dadi sosai.
2. Bread zaki samu, sai ki sami sardines ki farfasa shi, ki dan yanka masa albasa kanana a ciki, sai ki shafe a jikin bread din shima ki ki gasa shi a toaster. Amma a kiyaye shansa da tea mai madara.
3. A samu bread, sai a soya kwai, a sa a tsaki12795257_593277067506472_6087898731974255714_nyansa sai a rufe shima a gasa shi a toaster.
4. A samu bread a dafa kwai, sannan a samu shredded chicken (kaza wadda aka ma sala sala) sai ki dauko slice daya ki sa masa kwai dinnan bayan shima kin yanka sa slice, sai ki dauko bread ki kifa, sannan ki sake zuba shredded chicken dinnan a dayan ya zama step biyu kenan, shima sai a gasa shi.
5. Ki samu bread mai yanka yanka, idan wanda ba mai yanka yanka bane, sai ki sa wuka ki yanka shi yanda zai koma slice, sai ki je kitchen ki kada kwai, ki yanka masa albasa kanana, sannan ki sa masa maggi, sai ki sa mangyada a wuta, ki rinka tsoma bread din ya dibi kwai sosai, sai ki sashi cikin mai, amma shallow frying zaki yi ba deep frying ba. Shima yana da mutukar kosar wa, musamman ga yara masu zuwa school.
6. Ki samu bread ki cire gefe da gefe in da yayi brown kenan, sai ki yi egg sauce ki sa a ciki ki nandade gashi nan a cikin pictures. In kin so kuma zaki iya yi ta kwance, sai ki gasa abin ki.12140686_593277210839791_4661643856692050609_n
7. Ki fafe tsakiyan bread, ki sa frying pan a wuta, ki dauka bread din, ki diga mai ta dai dai tsakiyan da kika fafe, sai ki fasa egg a ciki ba tare da kin kada ba, ki sa maggi da salt da albasa ma in kina so, idan ‘kasa ya soyu sai ki kifa shi ko ina ya soyu. Idan ya soyu kwan zayyi kamar an dafa kamar an soya.

Sannan duka wainnan abubuwan zaki masa kwalliya ta hanyar yanka sa kamar sandwich, wato zaki kayata sa da yi masa kwalliya ta hanyar yanka shi irin shape na sandwich gasu nan a pictures.
Yar’uwar ku Sadeeya Lawal Abubakar.

Danna nan idan kana neman BIDIYON HAUSA masu ilimantar wa da NIshadantarwa musamman na Zamantakewa tsaknin Ma'aurata:


Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa

Updated: 2016-03-23 — 3:55 pm

2 Comments

Add a Comment
  1. Malama SADEEYA Ina maki fatan alheri, hakika kin yi kokari kuma dole a yaba maki wajen kawo labarin ki a kan biredi (bread), kuma labarin ki a tattare yake da ilimantarwa, wannan abun a yaba maki ne. Daga karshe nake mai baki shawar da ki rinka fasra wasu kalmomin misali: “Bread fast” da dai sauran su, dafatan ba za ki yi fushi ba. Nagode

  2. flnuqjhj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme