MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

AMFANIN GISHIRI shashida (16)

Gishiri yana da amfani da yawa bayan zubawa a cikin abinci, mutane da yawa sun zata amfanin gishiri shi ne kawai a zuba a cikin miya, amma ina, amfaninsa ya fi ga haka. Daga cikin nazarin da na gudanar, kwararru a fannin kiwon lafiya sun tabbatar cewa baicin abin da muka sani na al’ada, wato amfanin Gishiri cikin miya, hakikatan sun tabbatar cewa Gishiri dai yana da dimbin sirruka da amfani ga dan adam.  Kan haka ne, na dan zakulo muku kamar haka:

 1. Na farko, kowa ya san cewa idan Kyandir ya diga a waje, tilas zai manne da wajen, har sai an kankare shi da karfin tuwo, amma muddin ki ka jika Kyandir din ki na tsawon awa biyu ko uku, to da zaran kin kunna shi, yana ci, ko da zai diga a waje, ba zai kama ba. Za ki sha mamaki, domin da kin dan murje shi, zai fita, tamkar Kyandir bai taba diga wajen ba.
 2. Ina mata masu amfani da risho ko abin gashi irin na lantarki ko wanda ake amfani da Gas? Mafi yawan lokaci idan kina girki za ki ga ruwan girkin ko man gyada da ki ka yi suya da shi, ko dai wani abu da ki ka dafa a kan risho ya bata shi sosai, kafin kuma ki gama girkin ya bushe, don haka da rishonki ya fara baci sai ki barbada gishiri a wajen, da kin gama girki idan ya huce kina saka soso za ki ga ya fita. Haka ma za ki yi wa dukkanin ababen girkin ki.
 3. na uku, idan kina tababar kwai ko ya lalace ko yana da kyau, sai ki zuba gishiri karamin cokali biyu a cikin ruwa, ki kada, ki zuba kwan a ciki, idan yana da kyau za ki ga kwan ya yiwo sama yana yawo, idan kuma ya lalace ne kuma za ki ga ya yi kasa, sabanin abin da aka saba gani.
 4. Sosan wanke-wanke idan ba a tsaftace, shi sai ya zama waje ne da kwayoyin cuta suke dabdalarsu a ciki, don haka duk lokacin da ki ka gama wanke-wanke ki wanke sosan sosai, sai ki jika shi a cikin ruwan gishiri na awa daya ko biyu, kuma da zarar kin ga ya fara lalacewa ki yar da shi ki sayi wani, ba wani tsada ne da shi ba.
 5. Idan kin sayi tsintsiya kuma kina so ta dade miki, idan kin sayo tsintsiya kafin ki fara amfani da ita sai ki jika ta a cikin ruwan gishiri kafin ki fara amfani da ita.
 6. Idan zuma ta harbe ki, sai ki yi sauri ki zuba ruwan gishiri a wajen, yin hakan zai rage zafin harbin zumar, kuma wajen ba zai tashi ya yi ja ba.
 7. Amfani da ruwan gishiri mai dumi a lokacin da mutum yake fama da ciwon hakori da kuma ciwon makogaro yana kawo sauki, sai dai da kuna, idan kika daure kunar na wani lokaci ne, amma kafin jimawa za ki ga kin sami sauki.
 8. Ina masoya masu aikewa da junansu fulawa ko kuma masoya fulawa? Amma fulawar da nake nufi fulawar roba, na san ba kowa ne zai zauna ya goge fulawar ba idan ta yi datti ko kura, domin lungu da sakon da take da shi. Ki tsoma fulawar a cikin ruwan gishiri na ‘yan mintuna ki girgiza, dukkan dattin da ya ke jiki zai fita.
 9. Idan kina da madarar ruwa kuma tana saurin lalacewa, sai ki zuba gishiri dan kadan a ciki ki jijjiga ki rufe.
 10. Ina mashaya CAFE? Zuba gishiri dan kadan a ciki yana kara dadin NESCAFE din
 11. Idan jini ya bata miki kaya, sai ki jika su a cikin ruwan gishiri ki wanke, sannan ki saka su a cikin ruwan dumi da Omo ki wanke. Haka kuma idan gumin hammata ya bata miki kaya, sai ki zuba gishiri a cikin ruwan dumi ki wanke kayan.
 12. Ina ‘yan kwallo masu saka kanbas? Ga maganin hana takalmi wari. A barbada gishiri kadan a cikin takalmin sannan a goge. Amma takalmin kanbas kawai ban da takalmin da yake da leda ba, idan an saka a cikin takalmin da yake da leda gishirin zai ya lalata ledar takalmin.
 13. Kin sha kuka ne kuma ba kya so kowa ya gane ko kuma kin yi karatu tun da daddare har zuwa safiya, idanuwanki duk sun yi ja sun kankance, ga hanya mafi sauki da za ki yi amfani da ita domin idanuwanki su dawo su yi wasai kamar da. Ki zuba gishiri a cikin ruwan zafi ki gasa idanuwan da auduga.
 14. Ina mata ‘yan kwalisa masu son su ga fuskarsu ta yi fes, ki zuba gishiri da man zaitun a waje daya ki kwaba ki shafa a fuskarki, ki murza sosai domin ko ina ya ji, ki bar shi ya yi minti goma zuwa minti goma sha-biyar. Idan kika wanke zaki ji fuskarki ta yi laushi, idan kuma kina da kurajen ‘Taya-ni-muni’ ne zaki ga sun fara mutuwa saboda zafin gishirin. Idan kika dage da yi sau uku a sati ko sau hudu, za ki ga canji cikin kankanin lokaci.
 15. Idan kina da fararen kaya kuma sun dafe sai ki dafa su a cikin babbar tukunya na minti biyar ki zuba gishiri da bakin soda, idan kuma baki da babbar tukunyar da za ki dafa sai ki zuba gishiri da bakin sodar a cikin ruwan zafi ki zuba fararen kayan a ciki su jiku sosai.
 16. Haka kuma inda barkono, yaji ko attarugu ya shigar maki cikin idanu, da zaran kin dandana gishiri, radadin barkonon zai kau nan take kamar ba ki shafi yajin ba.

Danna nan idan kana neman BIDIYON HAUSA masu ilimantar wa da NIshadantarwa musamman na Zamantakewa tsaknin Ma'aurata:


Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa

Updated: 2017-04-23 — 9:11 am

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme