MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

BAN SAN DALILIN DA YA SA NA HANA NIGERIA BUGUN FANARETI BA – Alkalin Wasa

Alkalin wasan da ya duba gasar kwallon kafa ta Duniya da aka kara tsakanin Nigeria da Argentina ya bayyana cewa tabbas ya gani muraran sanda ɗan wasan kwallon Argentina, Mercus Rojo ya taɓa kwallo da hannu a wasan da ya gudana tsakanin Nigeria da Argentina ran Talatar 26-06-2018.

Amina Yusuf Ali

Kuma ya tabbatar da cewa taɓa Kwallo laifi ne ba wani ja a cikin al’amarin. Alkalin wasan ɗan asalin Turkiyya mai suna Cuneyt Cakin ya bayyana hakan ga shugaban kungiyar kwallon kafa ta ‘Super Eagles’, Mikel Obi. Bayan ya yi masa koken rashin adalci.

Nigeria da Argentina

Nigeria da Argentina

Cakin ya kara da cewa, sai bayan wasan sun sake duba bidiyon wasan ya kara tabbatar da Mercus ya taɓa kwallon a cikin minti na 82 da fara wasan kwallon. Amma ya ce shi har yanzu ba zai ce ga dalilin da ya sa bai ba da fanaretin ba.

AN BIYA YAN WASA TAWAGAR SUPER EAGLE NA NAJERIYA KUDADEN ALAWUS-ALAWUS DA SUKE BI

Ya yi kira ga ‘yan kwallon Nigeria da su ɗauki abun a matsayin kaddara. Kuma su tara i zuwa shekaru huɗu masu zuwa, ya san za su taka rawar gani. A nasa ɓangaren shi kuma Mikel Obi, yana ganin da an ba da wannan fanaretin ga NIgeria da watakila sakamakon wasan Nigeria da Argentina ya sauya.

Domin Kallon Sababbin fina finan Hausa Cikin sauka sai kuyi downloading App na Mujallarmu Tv a nan:
Download Mujallarmu TV (284 downloads)

Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa


Shiga Mujallarmu YouTube channel kayi subscribe domin kallon bidiyo da muka tanadar maka don nishadi da ilimantarwa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme