MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

Tag: Labarai

Masoya Buhari sun yi tir da kalaman Trump

Wata kungiya da ke mara wa Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari baya, ta yi watsi da kalaman da Shugaban Amurka Donald Trump ya yi, wanda wani rahoto ya ce ya bayyana Buhari a matsayin mara “mara karsashi”.

Kungiyar Buhari Media Organisation ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwar da ta fitar a ranar Talata: “Shugaba Muhammadu Buhari yana da cikakkiyar lafiya kuma zai shiga takara a babban zaben 2019. Kuma ya sake mulkar kasar na karin shekara hudu duk da kalaman Shugaba Trump,” in ji sanarwar.

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme