MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

YADDA JAMI’AN TSARO SUKAYI SANADIYAR ZUBEWAR CIKIN MATAR DAN TAKARAR GWAMNAN BORNO

Tsare Matar Dan Takarar Gwamnan Jahar Da Jami’an Tsaro Sukayi Yayi Sanadiyar Zubewar Cikinta

Daga Auwal M Kura
02/05/2018

Yanzu Haka Uwar Gidan Dan Takarar Gwamnan Jahar Borno Karkashin Jam’iyyar PDP, Girema Terab Ta Rasa Dan Cikin Dake Cikinta A Hannun Jami’an Tsaro,

Da Yake Tattaunawa Da Wakilinmu Dan Takarar Gwamnan Girema Terab Yayi Karin Haske Game Da Kama Matar Tashi Da’akayi, Inda Yace” A Ranar Sha Biyar Ga Watan Afirilun Wannan Shekara 15/04/2018 Bayan Sun Gudanar Da Wani taro Na Karawa Juna Sani Game Da Siyasar Dake Tafe Ta 2019, Wanda Kafin Suyi Taron Sun Rubutawa Kwamishinan Yan Sanda Wasika Cewa Suna Neman Goyon Baya Tare Da Hadin Kan Jami’an Tsaro Domin Gudanar Da Taron Cikin Kwanciyar Hankali Da Lumana Ba tare Da An Samu Wani Barazana Na Tsaro Ba,

Inda Rundunar Yan Sanda Da Ta Jami’an Sirri Ta Amince Sannan Lokacin Gudanar Da Wannan Taro Kwamishina Ya Turo Jami’ansu Shima Dpo Na Offishin Yan Sanda Dake Yankin Ja’e Da Aka Gudanar Da TaronShima Ya Turo Da Nashi Jami’an Don Ganin Anyi Taron Lafiya Angama Lafiya, Da Misalin Karfe Hudu Muka Fara Taro Sannan Muka Gama Da Misalin Karfe Shida.

Kuma Angama Lafiya Batare Da Wani Tashin Hankali Ba, Bayan Kowa Da Kowa Ya Watse Jami’an Tsaro Duk Sun Wuce Nima Bana Gida Sai Aka Kirani A Waya Ana Sanar Dani Cewa Ga Wasu Sunzo Da Wani Mutum Duk An Caccaka Mishi Wuka A Mace Sunyar dashi A Wajan Da Mukayi Wannan Taro , Ina Jin Haka Banyi Wata Wata Ba Nakira Jami’an Tsaro Na Sanar Dasu,

Bayan Sunje Sun Gudanar Da Bincikensu A Gurin, Daga Baya Sai Naji Kira Ana Shedamin Cewa Jami’an Tsaro Sun Tafi Da Mutanen Gidanmu Ciki Har Da Matata Dake Dauke Da Juna Biyu, ”

“Nayi Tinanin Dan Bincikarsu Za’ayi A Sakesu Amma Sai Naga Akwai Alamu Na Cin Zarafi Da Kage Da Akeso Ayimin, Wanda Sanadiyar Tsare Mai Dakina Da Firgici Yayi Sanadiyar Zubewar Cikinta, Inda Jami’an Tsaron Suka Kaita Asibiti Bayan An Tabbatar Da Cikin Ya Zube Sannan Suka Kara Komawa Da ita, Aka Tsare,Wanda Yanzu Haka Tana Bukatar Kulawa” – inji Girema Terab Dan Takarar Gwamnan Jahar Borno

A Karshe Girema Ya Roki Al-umma Dasu Saka Iyyalinshi Cikin Addu’a ,Kana Kuma Yayi Kira Ga Mahukuntan Kasar Nan Dasu Shiga Lamarin Don Ganin An Kwatarwa Wanda Aka Zalunta Hakkinsa, Sannan Allah Ya Tona Asirin Duk Wanda Yake Da Hannu Gurin Kulla Wannan Makirci

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Shafin Facebook
Shafin Twitter
Shafin Instagram
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: [email protected]

Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa


Shiga Mujallarmu YouTube channel kayi subscribe domin kallon bidiyo da muka tanadar maka don nishadi da ilimantarwa
Updated: 2018-05-02 — 5:02 pm

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme