SOJIJI SUKA TILASTA NI YIWA SHEHU SANI KAZAFIN KISAN KAI –GARBA ISAH

ANA WATA GA WATA: Sojoji Suka Tilasta Ni Yiwa Shehu Sani Kazafi — Garba Isa

Dan kato da Goran nan wanda ake zargi da kisan kai a Kaduna, Garba Isa ya yi ikirarin cewa sojoji ne suka tilasta shi kan ya yi wa dan majalisar Dattawa mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya, Sanata Shehu Sani kazafin cewa yana da hannun wajen kisan kan.
Ya ce ” na shaidawa sojojin cewa Ina daga cikin ‘Yankees kato da gora don haka babu yadda zan kashe wani, daga nan ne, suka fara lakada mani duka kan cewa dole in karba laifin kisan kan kuma cewa Sanata Shehu Sani ne ya umarce mu da yin kisan”.

Madogara:Rariya

This website uses cookies.