KASUWA AKAI MIKI DOLE. YADDA KASUWAR GARIN TALATA MAFARA DAKE JAHAR ZAMFARA KE CIKA DA MUTANE DUK SATI

Rahoto Na Mussaman

YADDA KASUWAR TALATA MAFARA KE CIKA DA JAMA’A DUK SATI A JAHAR ZAMFARA

DAGA AUWAL M KURA

Kasuwar Garin Talata Mafara Dake Dake Karamar Hukumar Fara Dake. jahar Zamfara, Kasuwace Da Akalla Ta Kai Sama Da Shekaru Dari Biyu Ana Gudanar Da’ita Duk Ranar Talata Na Kowani Sati ,Tsawon Shekaru Da Shekaru Komi Ruwa Komi Sanyi Haka Zalika Komi Zafi,

Kasuwar Ta Talata Mafara Ta Kasance Daya Daga Cikin Jigajagan Kasuwanni Da Manoma, Yan Kasuwa Sassa Daban Daban Na Arewacin Najeriya Ke Siye Ko Siyarwa A Cikinta , Sannan Ta Kasance Wata Jigo Ga Al-ummar Yakin Dama Jahar Zamfara Baki Daya.

Kasuwar Garin Talata Mafara Ta Shahara Gurin Saida Kayan Awo (Abinci) Dabbobi,Da Dai Sauransu, Bugu Da Kari Wannan Kasuwa Mai Limbin Tarihi Kabilu Daban Daban Da Suka Hada da Fulani,Hausawa,Yarbawa,iyyamurai Duk,Sukan Hallarci Wannan Kasuwa Domin Cinikayya.

Akalla Duk Sati Sama Da Mutum Dubu Goma Daga Sasssa Daban Daban Na Jahar Dama Kasar nan Ne Ke Zuwa Domin Cin Wannan Kasuwa Ta Garin Talata Mafara.

Ku Cigaba Da Kasancewa Dani Auwal M kura Domin Kawo Muku Rahotanni Na Mussaman Domin Haskaka Muku kan Al’adu ,Kasuwancu,Zamantakewa,Dama, Nishadi ,Harda Tarihi, Domin Fadakarwa,Nishadantarwa,Dakuma Samun Goge Da Daidai Ta Mu’amalar Rayuwa,

This website uses cookies.