DALILIN DA YASA ZA’A RATAYE WANI MATSHI A BAUCHI

An Yankewa Matashi Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya Bayan Kotu Ta Kamashi Da Laifin Kisa A Bauchi.

Daga Auwal M.Kura

Wata Babbar Kotun Jahar Bauchi A Ranar Jumma’a 11/05/2018 Ta Yankewa Wani Matashi Mai Kimanin Shekaru 33 Mai Suna Jaridu Ahmad Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya,

Katun Dai Ta Kama Jaridu Jaridu Ne Da Laifin Kashe Wata Budurwa Mai Kimanin Shekaru Sha Daya,Mai Suna Hajara Adamu, Sanan Ya Birneta A Dakinshi.

Da Yake Yanke Humuncin Mai Shari’aGurama Muhammad Mahmud Yace” bayan Sauraron Kowani Bangare Kotu Ta Kama Jaridu Da Laifin Aikata Kisan Kai Wanda Hakan Ya Sabawa Sashi Na 221 Na Miyagun Aiyuka Shafi Na 38 Mujalladi Na 3 Na Dokakin Jahar Bauchi Da Aka Sabunta Na Shekarar Dubu Biyu Da Bakwai(2007), Don Haka Kotu Ta Yankewa Jaridu Ahmad Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya “,

An Dai Gurfanar Da Jaridu Ahmad Ne A Gaban Kotu A Rana 30 Ga Watan Ogustan Shekarar Dubu Biyu Da Sha Biyar ,bisa Tuhumar Sa Da Kashe Wata Matashi Mai Suna Hajara Adamu tare Da Birne Gawarta A Dakinshi, Inda Yanzu Haka Kotu Ta Yanke Masa Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya Bayan Ta Kamashi Da Lafin na Kashe Matashiyar

This website uses cookies.