AN BINDIGE DAN TAKARAR SHUGABANCIN JAM’IYYAR APC

AN HARBE MAI NAEMAN SHUGABANCIN JAM’IYYAR APC HAR LAHIRA

Daga Auwal M Kura
6/05/2018
#JaridarTarayya

Wasu Yan Bindiga Dadi Sun Harbe Dan Takaran Shugabanci Jam’iyyar APC Na Gunduma Ta Goma(Ward 10) Mai Suna Jeremi III A Karamar Hukumar Ughelli Ta Kudu Dake Jahar Delta,

Mista Jeremiah Ogjoveta Ya Rasa Ransa Ne Daidai Lokacin Da Ake Gudanar Da Zabubbukan Gundumomi Na Shuwagabanni Na Jam’iyyar APC.
Kamar Yadda Bayanai Suka Nuna Makasan Sunyi Shigar Bazata Inda Kawai Sai Gawarshi Aka Gani Dauke Da Muggan Harbi A Jiikinsa

Mukaddashin Mai Magana Da Yawun Rundunar Yan Sanda Ta Jahar DSP Andrew Aniamaka ” Yace Har Yanzu Basu Samo Wani Rahoto Dangane Da Haka Ba Amma Da Zarar Ya Iso Garesu Zasu Sanar Da Manema Labarai Halin Da Ake Ciki.

©Jaridar Tarayya

This website uses cookies.