MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

[SIYASAR 2019] ZUWAN BUHARI KANO, BUKATA KO BORIN KUNYA?

Daga Mansur Ahmed

Kano garin da aka fi nunawa Buhari kauna, kano garin da aka fi bawa buhari kuri’a, kano garin da Buhari ya nuna a fili baya so “”

Na jima da cika da mamaki da Al’ajabin cewar gari kamar kano, jiha kamar Kano a wajen Buhari ace zai je Katsina sau 4 ya wuce zuwa Daura sau 4 amma ya kasa zuwa kano ko sau daya, yau har ya zama abun zolaya da mayar da mutumin kano wani sakarai wai Kaga ana bada sanarwar ku sa ranku a Inuwa Buhari zai zo rana kaza ko kaza

An yi gobara da ta zama sanadin karyewar arzikin dubban mutane, wadda ta jefa daruruwan mutane a masifa, ta raba su da sana’ar su, ta jefa wasu a rikicin rashin yadda zasu yi a Sabon Gari, Kwari, da sauran kasuwanni da ake alfahari dasu a fadin kasar nan Amma Buhari bai zo jajantawa Al’ummar da abun ya shafa ba

An gayyace shi bikin bude kamfanin sarrafa mai da yafi kowanne girma a Afrika da aka bude kwanakin baya a Kano bai halarta ba amma ya halarci bikin zagayowar murnar haihuwar mutane da kaddamar da littattafai, ya taya dan gidan Tinubu murnar ranar haihuwa yaje bukukuwa marar amfani birjik, yaje bikin bude kamfanin Olam a kaduna.

An jima ana cewa ba’a cika ganin Buhari a wajen binne gawa ko ta’aziyya ba duk kuwa kusancin dake tsakanin sa da mamacin. Mutane sun tabbatar da haka a rasuwar daya daga cikin manyan Aminansa (AVM Mukhatar Muhammad) bai iya zuwa jajensa ba duk kuwa da cewar zai iya hadawa biyu yayi nasa dana D’an Masani tunda ance mutuwa bata tsufa, kar mu manta Kungiyar TBO da ake tutiya da ita AVM ne yayi sanadin kafa ta, ya rike shugabanta daga baya ya zama mataimaki, Amma abota da Buhari bata yi masa rana ba

Har yanzu a Kano babu tuk’uicin aikin Biliyan 50 ko sama da Buhari ya kawo a matsayin Adashen da aka zuba masa, na tabbata akwai inda suka amfana da sama da haka a jihohin su Tinubu da Fashola,

Ko babu kyauta, akwai biyan bashi. Girma, martaba da darajar kanawa ta zarce irin wannan shakulatum b’angwaro da ake nuna musu. Yanzu idan ance zaka zo kano karshen watannan, ta’aziyyar rashe – rashen su MAGAJI DAMBATTA, YUSUF MAITAMA SULE, AVM MUKHTARI MUHAMMAD, INUWA WADA, da sauran manya zaka zo ko JAJENTAWA AL’UMMAR KANTIN KWARI, SABON GARI da sauran kasuwanni da suka fad’a iftila’in gobara, ko kuwa neman zub’in wani adashen ne aka fara zaka bud’e aiyyuka a saka sunan ka, ka fice sai kuma an kada gangar zabe???

Danna nan idan kana neman BIDIYON HAUSA masu ilimantar wa da NIshadantarwa musamman na Zamantakewa tsaknin Ma'aurata:


Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa

Updated: 2017-11-21 — 1:11 pm

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme