MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

RIKICHIN MANOMA DA MAKIYAYA INA MAFITA???

 

Daga. BILYAMINU SHUAIBU DANSADAU

MUSABBABI.
1.yawan wulakaci da rainin wayo da kabilar fulani suka fuskanta a shekarun baya ga mahukunta da da sauran alumma,
2. Zuba dabbobi a gonakkin manoma da fulani sukeyi da gangan,
3. Daukar hukunci ga hannu a tsakanin alumma,
4. Rashin daukar matakin gaggawa da gwamnati ya kamata ta yi idan matsalar hakan ta taso,
5. Mallakar haramtattun makamai da gwamnati ta ba ya wanzu ga alumma
6. Rashin kulawar gwamnati ga duka kabilun wato makiyaya da manoma
7. Rashin ilimi na addini da na zamani da ya mamaye kabilar fulani tun asali
8. Yin gonankki a saman hanyar makiyaya wato (burtali ko labi)
9. Kungiyoyin sa kai dake hukunci ba da sanin gwamnati ba.
10. Shigowar bakin haure miyagu suka bata na gida.
To da dai sauransu
HANYOYIN GYARA
1. Nuna soyayya da rage kyama ga kabilar fulani,
2. Samar da madatsan ruwa da hanyaoyi wato (burtali) ga su fulani
3. Kirkiro shiri don makiyaya ta hanyar ilmanatar da su da fadakarwa da su nemi ilimi da sanin darajar dan adam
3. Gwamnati ta kirkiro da numadic education sysistem ta hanyar jawo kabilar fulani ga jikinta
4. Daukar matakin gaggawa wajen magance rikichin da ya taso tsakanin manoma da makiyaya
5. Gwamnati ta kirkiro dabarun anshe haramtattun makaman da suka yawaita a hannun alumma,
6. Gwamnati ta kara azama wajen magance masu safarar miyagun makamai a kasar nan
7. Gwamnati ta sa idanu wajen bakin hauren da ke kwararowa a kasar nan ba izini,
8. Gwamnati tayi bakin kokarinta wajen ganin ta fidda iyakoki da hanyoyi wato (burtali) a tsakanin makiyaya da manoma,
9. Gwamnati ta kirkiro shirin yima fulani register ta hanyar gane yan kasa da bakin haure, wanda hakan zai bada damar gane fulanin kowane yanki a kasarnan.
10. Miyagun mutane suna amfani da kabilar fulani wajen cin karen su ba babbaka kasantuwar suna rayuwa ne a jeji, kuma basu da wadataccen ilimi da zasu fahimci hakan,
Don ALLAH duk mai wata shawara ya bada kuma kuyi SHIRE

Updated: 2018-03-23 — 10:55 am

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme