MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

MARTANI GA “YEMI OSINBAJO” MUKADDASHIN SHUGABAN KASA YA WARWARE ZAMAN GARGADIN DAYAYIWA ‘YAN AREWA AKAN KABILAR IGBO

Daga: ALI MUHAMMAD IDRIS (ARTWORK)

Ba tare da jinkiri ko gabatar da wani dalili da zaisa a fahimci sako na ba, cikin hanzari da kuma kudirin isar da sako na nake dauke da maganganu masu zafi da zasu tabbatar da kishina a matsayina na dan najeriya sannan dan arewa.
tun wata magana da matasan arewa suka fada ta harzuka shuwagabanni da sauran masu kishin kudu, dan bazan ce masu kishin najeriya ba. maganganun sun harzuka yawancin shuwagabanni da suka tabbatar da darajar yan kudu tafi darajar yan arewa, kalaman sun tabbatar da lallai yan kudu sune mutane, kuma sune masu najeriya dan mu yan arewa ba kowa bane illa dabbobin da suke kiwo, wadanda jahilci yayi mana kanta da kuma rashin sanin yanci. a karkashin rashin samun shugaba daya mai kishin mu ko shugabannin mu na arewa masu tsayawa kwato daraja da yancin mu a can.
Faruwar wannan lamarin yasa kai tsaye ana kokarin nuna cewa mu yan arewa mune masu tada husuma, mu mune bama son zaman lafiya, mu mune masu hargitsa najeriya. duk da basu da wani dalili daya da hakan ya taba faruwa, ni kuma kuma ina da tarin dalilai da zasu tabbatar da cewa yan kudu ko ince yan gata sune suke da abubuwan tada husuma. musamman kabilar IGBO
ina da tambayoyi masu yawa da zasu tabbatar da lallai wanene masu kokarin tada husuma.
shin su wanene suka fara maganar raba najeriya, wannan ba laifi bane?
shin su wanene suka fara gargadin wani yanki akan su tattara ya nasu ya nasu su koma yankinsu?
shin su wanene suke fasa bututun mai kuma su hana rayuwa mai dadi?
shin su wanene suke kashe yan wani yanki dake cikinsu wanda suka wa gargadi akan basu bar yankinsu ba?
shin a ina aka samu jagoran yan tada zaune tsaye NMAMDI KANU (jagoran kafa yankin BIAFARA) , wanda har bayan sakinsa da aka yi aka sa masa dokoki dan magance matsalolin da yake haifarwa.?
ko kun manta an gargade shi akan hada taro da ba zasu wuce mutum goma ba, shin ya daina? bayan kakkarya dokokin da kotu ta sa masa, har wani sabon gunkinsa aka yi dake nuna alamun girmamawa gare shi, wannan ya nununa alamu cewa yanzu suka fara. wannan ba laifi bane?

wadannan duk ba laifi bane? me yasa shuwagabannin mu na arewa basu taba daga murya dan kwatar yan cin wadannan yan arewa da ake zalunta ba? me yasa babu wani shugaba da ya taba hada taro dan a yi sulhu ba kamar yadda mukaddashin shugaban kasa OSINBAJO ya hada taro musamman saboda darajar yan kudu ba?

kai tsaye mukaddashin shugaban kasa ya hada taro da wasu daga manyan yan arewa da malamai dan tsaga gargadi ga yan arewa saboda an taba musu mutane, amma suna fakewa da cewa suna kokarin kawo zaman lafiya. anya idan zaman lafiya suke so su kawo ba taro ya kamata ayi da yan kudun da yan arewa a hadu gaba daya a yi sulhu a tabbatar da mai gaskiya da mara gaskiya a bashi ba? domin gudun abunda ka je ya dawo. me yasa aka yi taron banda su? ni a wurina hakan na nufin an shigar musu ne, ba tare da an gayyace su ba an tsaya musu an tsawatarwa da mu yan arewa da bamu san kanmu ba, da bamu da wadanda zasu shigar mana, da muka kasance bayi. a takamu a wuce.
Ina kira ga mukaddashin shugaban kasa, kamar yadda General muhammad Buhari ke kokarin kwatanta musu adalci duk da ba kabila daya ba, shima da ya janye kalamansa dan nuna muma yan arewa nashi ne. sannan hakan zai tabbatar da lallai yana son zaman lafiya ne, ba yana son wariya da nuna darajar bangare daya bane.
muna kiran shi ya sake gaggawar kiran zaman sulhu tsakanin shuwagabannin IGBO dana AREWA dan zama a yiwa kowanne bangare gargadi da kuma sa masa dokoki iri daya, babu wariya ko nuna kabilanci. hakan zai sa kowanne bangare ya tabbatar da ana adalci, kuma hakan ne zai sa muyi shiru, saboda munsan kuna son zaman lafiya.
sannan ya gaggauta sabunta gargadin da akawa NMAMDI KANU akan ya bi doka kamar yadda kotu ta bayar, ya dakatar da duk wani kudiri nasa na tada husuma. idan yaki a yi masa hukunci. shine zamu tabbatar da adalci ake so.
kamar kowanne lokaci ina tunatarwa cewa banyi rubutuna da nufin rashin biyayya ko kawo hargitsi ga kasata ba, saboda kowa yasan mu yan arewa munfi kowa son zaman lafiya, son zaman lafiyar ne ma yasa ni hango abunda zai iya faruwa idan ba ai gyara ba. dan haka zamu ci gaba da maida martani ga duk wanda baya kishin mu, kuma ba zamu fasa ba, saboda anyi walkiya mun gane.

DAGA dan arewa mai kishin arewa da najeriya baki daya.
ALI MUHAMMAD IDRIS (ARTWORK)

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Shafin Facebook
Shafin Twitter
Shafin Instagram
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: [email protected]

Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa


Shiga Mujallarmu YouTube channel kayi subscribe domin kallon bidiyo da muka tanadar maka don nishadi da ilimantarwa
Updated: 2017-06-15 — 10:39 am

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme