MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

KIRA GA GWAMNAN KADUNA MALAM NASIRU EL’RUFA’I DA SAURAN GWAMNONIN AREWA

DAGA ALI MUHAMMAD IDRIS (ARTWORK)

Akwai ingantaccen hadisin manzon Allah (s.a.w) da ya sanar damu cewa “idan muka ga abinki mu dakatar dashi da karfin mu, idan bamu da karfin mu dakatar dashi da bakin mu, idan hakan bai samu ba sai mu kyamaci lamarin a zukatan mu” sai ya kara da cewa “amma wannan shine mafi raunin imani”
Wasu abubuwa da suka yi kama da aikin jahilai da ke yawo a rayukan shuwagabannin mu na arewa. Suka tunzura ni nake so na isar da sakon dake raina wanda ban yiwa kaina alkawarin zan iya dauke kai suna faruwa ba. Duk da da dama daga cikin mutanen mu irina idan suka yunkuro zasu yi nuni kai tsaye sai a kira su da masu neman tada zaune tsaye, ko neman tada husuma. Kwatankwacin wani al’amari da ya faru a kaduna. Na wasu matasa da suke kungiyar matasan arewa suka tunatar da wasu yanki na kabilun kudu (igbo) cewa lallai sun basu watanni uku su tattara ya nasu ya nasu su koma garinsu.
Al’amarin ya mallakawa gwamnan kaduna Mal. Nasiru elrufa’i karfi da ikon sawa a kama su (a tunaninsa sunyi wani gagarumin laifin da suka cancanci haka)
Abunda nake so gwamnatin mu ta arewa da ta kaduna su duba shine.
Wace fuska maganar matasan ta nufa?
Menene manufa da ma’anar maganar?
Wane tasiri ne na maganar da ya zama cewa tada hankali ne?
Anya gwamnan kaduna yasan irin cin gashin dankalin da kabilar igbo kewa musulmai da duk wani dan arewa a kudanci kuwa? Anya yasan wulakantawa da kashewar da akewa mutanen mu na arewa mazauna can kuwa? Kodai Nigeria ba kasar dan arewa bace? Bashi da ‘yanci da ikon zama a ko’ina?
Me yasa shugabannin su na kudu basu taba kama wasu nasu da suke cutar da ‘yan arewa ba? Me yasa shugabannin mu basu mike sun kare martabar yan arewa dan hana su daukar mataki a hannu kamar yadda suke gani a yanzu sunyi ba?
A tsammanina idan da gwamantin arewa sun san cewa ana irin fiye da haka a kudu zasu fahimci inda kira da manufar wadannan matasa yake. Basa ganin kamar tunatarwa ce dan nemawa dan arewa ‘yanci a can kudu yasa su wannan maganar? Basa ganin wani abu ne da su ya kamata suyi dan mutunta wadanda suke tare dasu da kuma daraja ‘yan arewa dan a samu balance na zama lafiya a ko’ina ba?
Anya basu san hakan da suka yi na hukunta bangare daya illolin da zasu haifar ba?
Sun tabbatarwa da ‘yan kudu suci gaba da wulakanta ‘yan arewa kenan?
Sun tabbatarwa da ‘yan kudu ‘yan arewa ba ko’ina bace wurin zamansu kenan?
Tunda su sun kasa tsawatarwa da nuna abunda ya kamata suyi.
Akwai wani abu da nake so gwamnati da duk wani dan arewa su fahimta shine mufa ‘yan arewa ne kuma shuwagabannin mu na arewa mun zabe su ne dan kare martabar arewa, dan samarwa da dan arewa mutumci, dan kuma tsayawa a yiwa dan arewa adalci a duk abinda ya faru. Idan dakikin dan arewa yana maganar cewa ai gwamnatin ba ta dan arewa kadai bace to mu zauna mu zabi ‘yan kudun mana?
Mun zabe kune dan muna so kuyi koyi da tsohon gwamnan kano SANATA rabiu musa kwankwaso wanda shi kadai ne ya iya tashi takanas ta kano ya isa ILE IFE ya tsawatar irin tsawatarwar da bata saba doka ba, kuma ta dago daraja da mutuncin yan arewa.
Lallai irin albishirin da yayi cewa idan aka ci gaba da yiwa yan arewa wulakanci suma aka kaisu bango suka yunkuro suna tsammanin kasar zata zauna lafiya ne? to babbar masalaha idan irin wannan al’amarin ya faru shine a yi hukunci na gaskiya, a duba kowanne bangare a basu rashin gaskiyar su da gaskiyarsu. Amma daga cikin wasu lalatattu marasa kishin arewa sai suka ce ya shigo da siyasa, ni a nawa ganin wannan shine hakkin daya rataya a gun shugaba dan arewa. Kamar yadda suma idan wani abu da ya faru suke tsayawa su ga sun kwato musu yanci. Kamar wani abu daya faru a kano akan wata mata yar kudu datayi batanci… matasa suka kashe ta. sai da wasu shuwagabannin su na kudu suka tsaya saida aka biya diyyar wannan matar. Me dan arewa zaka kira wannan abun idan ba kishi ba?
Yanzu an kama matasan arewa su kuma can ba a tsawatar musu ba me hakan yake nufi? Yana nufin an basu kofar ci gaba da wulakanta yan arewa, mu kuma an rufe mana baki mun kasa Magana?
Idan an hana mu Magana, to wane shugaba zai iya tsayawa a kudun ya tsawatar musu, ya dago darajar matasan mu?
Wannan mulkin yana so yayi kama da mulkin mallaka… dan adam bashi da ‘yancin yin Magana ne idan an cutar dashi, musamman dan arewa?
Shirun da muke yi ta dalilin tsoron kada a kama mu ko a hukunta mu shine yasa ‘yan kudu suka raina yan arewa, saboda shugabannin sun riga sun jefa tsoro a zukatan yan arewa. Muna son zaman lafiya amma bamu yarda shugabannin mu su kasa tsayawa su zama bango da kafafun mu ba.
Yanzu rainin har ya kai fariyar a raba kasa a wurin yan kudu.
Abunda yake sa ‘yan kudu surutu da karfin halin cewa a raba kasa saboda sune suke da man fetur, shin sun manta ne.. arewa fa ba kasar talauci bace, mune muke da duk wani arziki idan ka dauke man fetur da najeriya ta jingina dashi. Ko sun manta mulkin duk da aka yi a najeriya basu kai yan arewa yi ba? Ko sun manta gyada da auduga sun daga darajar najeriya suka kaita inda har ake iya gane najeriya a sahun kasashe?
Daga karshe ina kira ga gwamnati da talakawan arewa, wallahi mu farka mu tuna cewa najeriya kasar muce. Kuma idan tura ta kai bango al’amarin bazai yi kyau ba.
Sannan ina tunatarwa cewa mu ba masu nufin tada zaune tsaye bane. Ba nayi rubutun nan dan tunzurawa ko haifar da wani abu ba face tunatarwa kamar yadda Allah (SWA) Yace “ku tunatar, domin lallai tunatarwa tana amfanar da mumini”
Zamu ci gaba da yin biyayya ga shugabanni in har sun tsaya mana suka daraja darajar mu.
Daga: ALI MUHAMMAD IDRIS (ARTWORK)

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Shafin Facebook
Shafin Twitter
Shafin Instagram
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: [email protected]

Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa


Shiga Mujallarmu YouTube channel kayi subscribe domin kallon bidiyo da muka tanadar maka don nishadi da ilimantarwa
Updated: 2017-06-08 — 4:37 pm

1 Comment

Add a Comment
  1. Lallai wannan shine since nagaskiya tunda such manyanmu summaidamu tumaki yakamata mununa musu mumazamu iya karbowa kanmu yanchi shekara nawa akekashe mana mutane gamma bawanda yayi tir I banda kwankwaso gamma sai dan ambasu waadinbarinyankinmu ace bamuyidaidaiba Ai wan an ma adalcine wallahi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme