MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

KARANTA KAJI: SUNNONI 10 NA MANZON ALLAH (S.A.W) DA AKE SON MUSULMI YAYI KOYI DASU RANAR IDI

Garabasa: Sunnah 10 na Manzon Allah SAW a Ranar Idi.

Marubuci:Haruna Sp Dansadau

Musulmai na shirin murnar karamar Sallah a Duniya Da zarar Azumi ya kare za ayi biki a Duniyar Musulmai  akwai sunnoni da dama a wannan rana da ya kamata a kiyaye Bikin Sallah.

Sarkin Musulmi a Ranar Idi Dandalin Mujallarmu.com ta kawo maku wasu sunnonin Manzon Allah a matsayin garabasar wannan shekara.

1. Wankan tsarki Ana bukatar wankan gusul kafin a je Masallacin Idi

2. Karin safe Yana cikin sunnah a samu wani abinci a tauna kafin a tafi Masallacin Idi a lokacin karamar Sallah.

3. Sababbin kaya Daga cikin Sunnah ana so a sanya sababbin kaya a Ranar Sallah ko kuma mafi kyau akalla

4. Sallar Nafila Bai halatta ayi Sallar Nafila a filin Idi ba yayin da ake jirar Liman.

5. Nafila a gida Ana kuma so ayi nafila raka’a 2 rak yayin da aka dawo daga Masallacin Idi watau a gida.

6. Sauya hanya Yana daga cikin Sunnah a canza hanyar da aka bi wajen zuwa yayin da ake dawowa gida

7. Takawa a kafa An so a je Masallaci a kafa ba bisa wani abin hawa ba domin zuwa Sallar Idi.

8. Gaisuwa Sahabbai kan gaida ‘Yan uwan su yayin da su ka hadu domin murna a wannan rana.

9. Ziyara Ziyarar ‘Yan uwa da abokan arziki na cikin Sunnah a wannan lokaci na farin ciki.

10. Kabarbari Ana fadan Allahu Akbar, Allahu Akbar, La ilaha illalLah, Allahu Akbar, Wa lilLahil hamd. K

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Shafin Facebook
Shafin Twitter
Shafin Instagram
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: [email protected]

Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa


Shiga Mujallarmu YouTube channel kayi subscribe domin kallon bidiyo da muka tanadar maka don nishadi da ilimantarwa
Updated: 2017-06-20 — 6:23 pm

1 Comment

Add a Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme