IRIN ZAMBA CIKIN AMINCI DA GWAMANAN JAHAR ZAMFARA YAYI WA TALAKAWANSA DA BASU LURA BA

A hakikanin gaskiya Gwamnan Jahar Zamfara na daya  daga  cikin gwamnonin Najeriya da suka shimfida tituna.

Duk da yake a karonsa na biyu kenan akan karagar mulki, zamfarawa da dama zasu aminta cewa yayi aiki sossai ta wannan bangaren.

Sai dai  kuma wane IRIN aiki ne ake yi a nawa  akeyin aiki?

Abunda ya janyo hankalina shine a cikin kwana Dari da hawansa mulki yayi aikin titin Bye pass dake  babban birnin Jahar Gusau sai gashi kuma yanzu naga ana sake shimfida wani titin.

Ina ganin ya kamata Zamfara su farga su gane  cewa akwai yiyuwar wasu da akayi kamin wata gwamnati ta wuce sai an sake maimaitasu domin kuwa wannan ya nuna  ba ayukan kwarai ake muku ba.

Allah sanyawa shugabanin mu tausayin mu a ransu.

This website uses cookies.