DALILIN DA YASA MUKE BUKATAR MATASA MASU ILIMIN ZAMANI A MATSAYIN SHUGABANIN MU A NAJERIYA

A duk lokacin da naji matashi yace BA MATASA BANE MAGANIN MATSALAR NAJERIYA sai inji wannan matashin bai san me ake bukata wajen Gyaran Najeriya ba.

A koda yaushe muna zaunawa muna tattauna matsalar Najeriya amma kadan daga cikin mune zakaji suna magana akan mafita. Kusan duk wata mafita da zakayi tunani zakaga akwai wani abu da zai hana ta yiyuwa.
Wani mahimmin abu da ya kamata mu sani shine matasa suke da ilimi na zamani wanda ake bukata a wannan zamani. misali Ilimin Na’ura mai Kwakwalwa wato Computer dana Information Technology. Duk wata kasa da kaga sunci gaba irin wannan ilimin suke amfani dashi wajen magance matsaloli daban daban musamman tsaro, da cin hanci da rashawa.
Muddin bamu maida hankali akan amfani da wannan ilimin ba abubuwa da dama bazasu taba gyaruwa ba a kasar nan musamman rashawa.

This website uses cookies.