MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

DALILAN DA YASA KUDANCIN NAJERIYA SUKAFI MU CI GABA

Kamal Saidu Dansadau

 

Nasan mafi yawancin Jama’ar yankin Arewacin Najeriya zasu yadda da wannan kalami Nawa dukda Nasan bazaa rasa wasu da zasu ga hakan ba gaskiya bane amma Ina so Mai karatu ya fahimci dalilai na musamman na farko.

Har yanzu Arewacin Najeriya mun kasa Haka kanmu daga sama Har kasa, Musamman mu na kasan. Babu yadda alumma zata iya ci gaba idan Babu hadin Kai. Da Zamuyi kokarin hada kanmu da sai munfi fahimtar abubuwan dake faruwa a Najeriya musamman a siyasance.

Akwai matsalar rashin ilimi sossai a Arewacin najeriya kuma hakan yasa bamu da masaniya akan abubuwa da dama da zasu amfanemu. Da gangan yan siyasa basu son ilimi ya yawaita saboda kada wasu assiransu su tonu. Da zamu rika neman ilimi musamman na Addini kuma muyi amfani dashi kamar yadda ya kamata Wallahi Babu wanda zai iya nuna mana ci gaba.

 

Mun maida siyasa tamkar Addini da wajen neman kudi kuma hakan Babban kuskure ne. Da Matasan Arewa zamu maida siyasa wani abu mai zuwa ya wuce cikin kankanin lokaci kamar yadda yan kudancin najeriya sukeyi da baza mu taba zama cima kwance ba.

A arewacin Najeriya ne kawai zakaga dan siyasa ya dauki matasa aikin yi masa rubuce rubuce a social media. Bayan matashin ya tabbatar da abunda yake tallatawa ba abun kwarai bane kuma ba Gaskiya bace yake fadi.

A kudancin najeriya duk abunda Gwamna yayi Ko wani Dan siyasa zakaga Kowa ya fito ya sa albarkacin bakinsa Badan wani Ya biyashi kudi ba, amma mu a Arewa sai muce idan Shugaba yayi ba daidai ba Bai kamata ayi magana Ba wannan kuskure ne.

Ko Sayyidina Umar RA ya saurari korafe korafen talakawan sa a lokacin da yake mulkinsa. Amma Babu inda musulunci yace ka zagi Shugaba idan baiyi daidai ba Koda ba musulmi bane.

Ina kira da yan Arewa da mu cire son zuciya mu nema mafita Domin kuwa an barmu a baya bayan kuma Koda turawa suka zo sun same mu masu ilimi.

 

Allah ka bamu ikon gyarawa ka kuma bamu shugabanni masu tausayinmu

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Shafin Facebook
Shafin Twitter
Shafin Instagram
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: [email protected]

Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa


Shiga Mujallarmu YouTube channel kayi subscribe domin kallon bidiyo da muka tanadar maka don nishadi da ilimantarwa
Updated: 2018-03-07 — 10:26 am

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme