MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

BA ARATABU AKAYI DA YAN SHI’A BA YAU A ABUJA

Taya Za’ace Artabu ?

Tsakanin Mabiya Akidar Shi’a Da Jami’an Tsaro

Rubutawar: Auwal M Kura

Maganar Gaskiya Shine Yana Da Kyau Masu Dauko Rahoto Da masu Bugashi Sukasance Masu Daukar Gaskiya Tare Da Bugawa Gaskiya Ba Tare Da Nuna Banbanci Akida Yare ,Addini Ko Launi Ba.

Na Danyi Wannan Tsokaci ne Bisa Abun Da Ya Faru Tsakanin Mabiya Hakidar Shi’a Da Kuma Jami’an Tsaro Yau A Babban Birnin Tarayya Abuja.

Kamar Yadda Da Yawa Daga Cikin Kafafen Yada Labarai Kan Cewa Anyi Artabu Tsakanin Mabiya Akidar Shi’a Da Jami’an Tsaro , Maganar Gaskiya Ba Haka Rahoton Yake Ba Domin Kuwa Babu Yadda Ace Anyi Artabu Tsakanin Mutumin Dake Rike Da Kwalli Da Kuma Jami’an Tsaro Dake Rike Da Bindiga Da Motoci, Wannan Sam Bazai Yuwu Ba.

Maganar Gaskiya Shine Ba Artabu Akayi ,An Samu Rashin Fahinta ne Kuma Daga Baya Jami’an Tsaro Sukayi Amfani Da Karfinsu Wajan Tarwatsa Mabiya Akidar Shi’a Lokacin Da Suke Dauke Da Kwallayen Nuna Rashin Goyon Bayansu Ga Gwamnati Bisa Cigaba Da Takeyi Na Tsare Malaminsu Kimanin Shekaru Uku Ba Bisa Ka’ida Ba.

Jan Hankali, A Matsayina Na Mai Aikin Yada Labarai Da Rahotanni Nauyine Akaina Fadin Gaskiya Kan Kowa Ba Tare Da Nuna Banbancin Ba Kamar Yadda Aikin Jaridanci Ya Tanadar, Haka Kuma Masani A Aikin Jaridanci Na Duniya Dan Kasar Indiya Farfesa Sharma Ya Kara Tabbatar Da Hakan Cikin Littafinsa mai Suna( Editorial And Reporting In Journalism) a Turance , Don Haka Banyi Wannan Rubutu Domin Goyon Baya Ko Kuma Kuntatawa Wani , Aa Tsabar Gaskiya ce Data Wajaba Na Bayyana Domin Saukr Nauyin Dana Daukar Ma Kaina

Updated: 2018-04-16 — 5:16 pm

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme