MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

ABUNDA NA HANGO SHEKARU BIYU, ZAI FARU GA MATASANMU A ZAMFARA, YA TABBATA GASKIYA A YANZU!

Shekaru biyu da sunka wuce baya, na sha rubuce-rubuce akan abunda na ke hango ma, mu Al’ummar Jahar Zamfara. Sakamakon rikon sakainar kashin da gwamnatin Jahar Zamfara karkashin jagorancin Gwamna ABDUL’AZIZU ABUBAKAR YARI MAFARA. Ke yiwa matasan jahar tare da nuna halin ko in-kula akan makoma ko halin da matasan za su samu rayuwarsu!

 

Na tabbatar matasa su ne kashin bayan cigaban kowace Al’umma kuma duk Al’ummar sunka rasa samun nagartattun matasa to take Al’ummar za ta wargaje. Wannan kenan.

 

Duk Bazamfare da ke numfashi a jahar Zamfara tare yin tataccem tunane. Zai tausayawa matasan jahar. A halin da mu ke ciki yanzu.

 

Na tabbatar nauyi ne ya rataya kan uba na tabbatar da cewa ya kula da ci sha, Tarbiya da kuma dora iyalin akan turba ta gari, sauran sai ya bar wa mai ni da ku ya shirya masa.

 

Haka zalika nauyi ne, ya rataya ga kowace Irin Gwamnati na kula da rayukka da dukiyoyin mabiyanta. Tare da tabbatar da jin dadi da walwala na Al’ummar Dan tabbatar da cewa mabiyan sun zama masu zurfin tunane da nuna kishin kasa da ita kanta Gwamnatin.

 

Sai dai kash! Abun ba haka ya Ke ba, a Jahar da Allah ya nufi zan tashi kuma yanzu na ke rayuwa a cikinta.

 

Domin An wayi gari kwata-kwata Gwamnatin Jahar ba ta kula da matasan Jahar ba. Ta hanyar tabbatar da ba su ilimi ingantacce, balantana Tarbiya wanda tuni shari’ar da mu ke kuri da ita ta zama Tarihi, barna da masifaffiyar caca ta dawo. Wadda mun yi kukan a dauki mataki Tun kafin ta karbu. Amma anki, yau cacar ta game dukkanin matasan jahar Musamman na Gusau. Wanda ya haifar da Karin mutuwar zuciya da neman Haramun Ido rufe.

 

Tuni dai tunanenmu na samun damar aikin yi koda kuwa Na hannu ne daga tallafin gwamnatin  da munka Kira ta dimokadiya!  ya kau a zuciyoyinmu. Domin ta rufe Dukkanin cibiyoyin koya muna sana’o’in hannun da ta gada daga Gwamnatocin bayan. Haka tun bayan da gwamnatin ta hau mulki yau sama da shekaru shida, ba taba Daukar matashin Jahar aiki a cikin ma’aikatun Gwamnatin jahar ba. Duk da kullum ma’aikatanta na mutuwa, ritaya wasu kuma sun bar aikin bayan sun samu wani aiki na tarayya.

 

Maganar a taimaki matasan jahar su yi karatu, wani Tsohon al’ammari ne, da ya zama tarihi a kundin Jahar. Wanda hakan ya haifar da mummunar lalacewar ‘yan uwa matasa. Saboda da haka matasan jahar zamfara suke ta yin HIJIRA zuwa makwabtan jahohinmu tare da barin kasar wajen ginar zinari a haramtacciyar hanya. Duk dan rayu kada yunwa ta yi masu Illa.

 

Wanda lokacin da matasanmu sunka Fara yin HIJIRA zuwa Janhuriyar Nijar ginar zinari a haramtacciyar hanya. Na yi ta rubuce-rubuce akan babbar illar da hakan zai haifarwa Zamfarawa. Wanda a lokacin na nusar da Gwamnatin ta kula. Na ce na tabbatar ba ta yi daukarmu aiki mu duka, amma ta inganta hanyar samar muna da ilimi tare da saukaka muna shi, ta yi kokarin ganin cewa ta tallafawa masu son zurfafawa karatunsu ko da kudi kalilan ne, zai taimaka wajen Kara muna karfin guiwar cigaba da Nema. In mun Kare ta yi kokarin daukar wasunmu aiki, Mai son kasuwanci ko kalilan ne, ta tallafa masu. Haka zalika wadanda ba su cigaba da karatun ba a koyar da su aikin hannu na ainihin da babu siyasa cikinsa, Wanda zai sa mu dogara da kanmu har mu taimaki wasunmu.

 

Haka zalika a lokacin na kallo Irin miyagun dabi’u da matasan za su koyo a can, tare da masifar da sabon da za su da kudi wanda watan wata rana za a rufe hanyoyin neman. tunda ba tattali sunka iya ba, na hannunsu za su Kare, sabo turken wawa ya shiga, ba bagiren neman a Zamfara. Wanda hakan zai haifar da sace-sacen kayan mutane.

 

Allah mai girma Dukkanin wadannan hasashen nawa yau sun zama Gaskiya. Yau a jahar Zamfara mafiya yawan matasan da sunka bar kasar zuwa Nijar hakar zinari ta hamtacciyar hanya da mu ke kira “‘YAN ARLET” su ne babbar masifar da ke biyar garuruwanmu Musamman babban Birnin Jahar wato Gusau. Domin mafiya yawansu son koyo zinace-zinace a can tare da kwaso Ciyo mai karye Garkuwar jiki. Bugu da kari duk ka ga gungun matasa suna masifaffen gudu da babura a garin Gusau to matasan ne, wanda kullum sai sun buge mutane wasu su Kare, wasu su samu mummunar rauni! Wanda ko shekaranjiya sun buge wani Jami’in Tsaro. Haka zalika yanzu da na ke wannan rubutun Wallahi sun buge wasu magidanta, Dukkaninsu sai da sunka samu raunukka.

 

Haka ko kwanakin baya an Kama wasu barayi da satar babura tare da Balle gidajen al’umma, wadanda anka tabbatar da cewa ‘yan Arlet ne. Sai kuma Mummunan halin da garin Gusau ya Ke ciki duk da wannan Matsalar ba jahar Zamfara dai ta ke fuskanta ta ba. Wato kwatar wayoyi a hannun Al’umma. Wanda an tabbatar da cewa itama ta’asar ‘yan Arlet din ce.

 

Sai dai duk da haka, ba ta sanya Gwamnatin Jahar Zamfara ta shiga cikin hayacinta, na Daukar matakin magance wannan Matsalar ba. Hasalima hanyoyin da za su Kara jefa Al’ummar Jahar Musamman matasan Jahar cikin tashin hankali ne Gwamnatin Jahar ta dauka.

 

Domin a ranar Assabar 7-10-2017 Gwamnatin Jahar ta fitar da Sanarwar dena hawa babura daga karfe goma na dare zuwa 6 na safe, wai a cewarsu shi ne matakin magance Matsalar sace-sacen da ke addabarmu.

 

Wanda kamar yadda mu ke gani sanya wannan dokar baya ga kashewa wasu matasan da ke kokarin neman abinci ta hanya mai kyau da ya yi. Garuruwanmu za su Fara yi tsit! ne da wuri. Wanda Barayin kanyi amfani da damar domin balle Shaguna cikin salama tare da yin ta’asar cikin kwanciyar hankali. Ko ba komi akwai matukar karancin jami’an tsaron kwata-kwata a jahar, wanda duk Najeriyar ce, haka. Balantana har a samu wadatattun jami’an da za su cigaba da zirga-zirgar a cikin daren. Duk da kullum cikin kuka su ke cewa babu Mai motocinsu.

 

Dan Haka Shawarata ga Gwamnatin Jahar Zamfara karkashin jagorancin Gwamna ABDUL’AZIZU ABUBAKAR YARI MAFARA, ita ce; da farko dai ya ji tsoron Allah, wannan mulkin da Allah ya ba shi kamar gobe ne, zai Karbe abunsa. Dan haka ya yi kokarin inganta rayuwar matasan jahar ta hanyar taimakonsu, ta kowane hauji. Wanda Samar da aikin yi gare su ne zai kawo karshen Matsalar, amma Wallahi muddun anka tafi haka to Shakka babu mu matasa da ke karkashinka, Wallahi za mu yi Allah waddai da Kai ne, tare rokon Allah ya yi maka yadda ka yi muna. Domin dai yayanka duka babu wanda zaka iya bari ya shiga halin da sakacinka ya sanya mu ciki.

 

Daga karshe ina Rokon Allah shirya muna shuwagabanninmu, ya albarkaci rayuwar matasan jahar, ya yi muna gata tare da kawar muna da kowane Irin shugaba da ke da zummar jefa rayuwarmu cikin kunci! Ya Allah yanzu mu ke tsakkiyar kurciyarmu, rayuwarmu ta ke cikin Tsaka mai wuya, gyaruwarta da bacinta duk a yanzu take, ya Allah gyaran da bacin duk naka ne. Ya Allah ka albakaci rayuwarmu duniya da Allah. Allah duk Wanda ke biyarmu da bakar yadiya Allah ka mayar masa da abarsa.

 

Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau (Jami’in Hulda Da Jama’a Na Kungiyar Muryar Talaka Reshen Jahar Zamfara) 08069807496

 

9-10-2017

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Shafin Facebook
Shafin Twitter
Shafin Instagram
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: [email protected]

Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa


Shiga Mujallarmu YouTube channel kayi subscribe domin kallon bidiyo da muka tanadar maka don nishadi da ilimantarwa
Updated: 2017-10-09 — 5:57 pm

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme