MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

SIRRIN DA NAMIJI: HANYOYIN SAKA MAI GIDA FARINCIKI – UMMULKHAIR

Sirrin da namiji: Na yi bayanai sossai a baya akan yadda zaki kula wajen samun miji na gari da yadda zaki kula da wajen bashi hakkin shi a matsayinshi na mijinki.

A bayanin yau zan su in fahimtar da yan uwana mata akan yadda zaki rika saka mai gida farin ciki, domin abu ne mai mahimmanci a rayuwar Aure. duk da yake kowa da irin yadda Allah ya halicceshi amma akwai wasu abubuwanda ya kamata ki kula dasu.

Abu na farko shine me musulunci ya tanada ma Ma’aurata? duk wani abu da zakiyi a zaman aure ki tabbatar da kinyi shi akan tsarin musulunci, kada kiyi sabon Ubangiji domin kina so ki farantawa maigida rai. Yin hakan zai sa Allah ya sa masa natsuwa da farin ciki a rayuwarsa wanda kuma kece sila.

Abu na biyu shine ki kula wajen masa irin abubuwanda yake so, musamman bangaren Abinci, da kuma Kwanciyar sunna. Mata da yawa basa damuwa da wannan bayan kuma abu ne mai mahimmanci sossai a Zaman Aure. Ki tabbatar da kinsan abunda yake so.

Sannan kuma abu na karshe da zan bayyana shine Ki rika Masa Addua musamman idan zai fita zuwa kasuwanci ko aiki. sannan ki rika Ibada domin idan kika kasance mai ibada mijin ki zai samu natsuwa da farin ciki a tare da shi koda shi ba mai yi bane.

Allah yasa mu dace ya Bamu zaman Lafiya da Mazajen mu.

Amin

Ummulkhair Hayatudden

Danna nan idan kana neman BIDIYON HAUSA masu ilimantar wa da NIshadantarwa musamman na Zamantakewa tsaknin Ma'aurata:


Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa

Updated: 2018-06-16 — 6:15 pm

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme