MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

SHAWARWARI 52 DA ZASU KARA KAUNARKI DA KIMARKI A GURIN MUJINKI

SHAWARWARI 52 DA ZASU KARA KAUNARKI DA KIMARKI A GURIN MUJINKI

SHAWAR WARI HAMSIN DA BIYU DAZASU KARA KAUNARKI A ZUCIYARA MIJINKI

SHEIKH JA’AFAR MAHNUD ADAM
Arewatimes.com.ng

Arewa times:
1-Aurenki ya zama domin neman yardar ALLAh kikayi ba dan tara abin duniya ba.

2-Kada ki zama mai kwadayi wajen zaben mijin Aure.

3- Ki zabawa ‘ya ‘yanki uba ta hanyar Auren wanda ki ka yarda da addininsa da dabi’unsa harma da dangantakarsa.

4- Ki zama mai riko da addini a gidan mijinki.

5- kada ki zama mai kauracewa shimfidar mijinki.

6- Ki zama mai hakuri da halayyar mijinki.

7- Ki zama mai matukar biyayya ga mijinki.

8- Ki zama kwararriya wajen iya kwalliya kala-kala.

9- Ki zama kwararriya wajen iya girki kala-kala.

10- Ki zama kin iya barkwancin magana wajen baiwa mijinki dariya.

11- Kada ki zama mai rainuwa a cikin duk abinda mijinki ya baki.

12- Ki dinga wanke bakinki da safe da yamma da kuma lokacin kwanciya barci.

13- ki zama mai tsaftar jikinki, gidanki, abincinki, da sauransu.

14- Ki dinga girmama Iyayan mijinki da ‘yan uwansa da abokansa.

15- Kada ki zama mai satar kayan mijinki.

16- Kada ki zama mai satar fita unguwa.

17- Ki guji Leke a gidan mijinki, dan yana daga cikin abinda yake raba Aure a tsakanin Hausawa.

18- Ki dinga godewa mijinki a cikin abinda ya baki.

19- ki kiyaye abinda mijinki ya fi so.

20- ki kiyaye abinda mijinki ya fi sonci da safe, rana, dakuma dare.

21- Ki dinga yabawa mijinki kwalliyarsa.

22- Ki dinga yawan neman shawarar mijinki akan duk wani al’amari da zaki yi.

23- Kiyi kwalliya ki tsane tsaf kafin dawowar mijinki.

24- Ki dinga sanya turaren wuta a dakinki, kuma ki kasance mai sanya turare a jikinki a duk lokacin kwanciya.

25- Lallai ki yi kokarin gama aikace-aikacenki kafin dawowar mijinki.

26- Kada ki bari mijinki ya dawo ya sameki gaja-gaja, ki sani kazanta tana haifar da kiyayya.

27- Ki zama mai yawan canza zanen kunshin kafarki da kuma zanen kitso.

28- Kada ki ce mijinki sai ya saya miki abinda ba shida ikon saye.

29- Lallai ki yi amfani da ilimi wajen yanke dukkan wani hukunci.

30- Ki yi shiru a duk lokacin da mijinki yake yi miki fada ko Nasiha.

31- Kada ki zama Al-mubazzara mara tattali.

32- Kada ki tara kayan wanki da yawa a daki, naki ko na mijinki suna wari.

33- Ki tanadi kayan kwalliyar gida bayan na zuwa unguwa.

34- Ki kula da yanayin da zai nuna miki cewa mijinki yana cikin Nishadi ko Damuwa.

35- Kada ki ringa baiwa kawayanki labarin sirrin dake tsakaninki da mijinki.

36- Idan zaki yiwa mijinki magana kiyi masa da tattaunsan harshe, da murya mai karya zukata.

38- Ki zama kin iya kallo mai nuna alamun sha’awa ko soyayya.

39- Idan kika samu sabani da mijinki ki bashi hakuri ko da kuwa kece da gaskiya.

40- Ki zama mai tattali a cikin dukkan abinda kika mallaka a gidan mijinki.

41- Kada ki zama mai kwauron baiwa dangin mijinki abinda ya umarceki da a basu.

42- Kada ki zama mai yin dare wajan girki.

43- Kada ki zama uwar adashi ba tare da sanin mijinki ba.

44- kada ki zama mai yawan fada da makwabtanki.

45- Kada ki kasance mai yawan zagi ko Ashariya.

46- Kada ki ringa baiwa Iyayanki Labarin laifin da mijinki yake miki.

47-Ki zama mai hakuri da juriya da halayyar Iyayan mijinki da ‘yan uwansa.
48-Idan mijinki ya yi miki laifi kada ki nuna masa bacin ranki a gaban iyayanki ko ‘yan uwansa.

49-Kada ki ringa daga murya sama idan kuna sa-in-sa da mijinki.

50-Kad ringa baiwa ‘yan uwan mijinki labarin laifukansa.

52- Ki dinga yiwa mahafiyar mijinki Ihsani da ‘yanuwansa

Danna nan idan kana neman BIDIYON HAUSA masu ilimantar wa da NIshadantarwa musamman na Zamantakewa tsaknin Ma'aurata:


Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa

Updated: 2018-05-18 — 10:55 am

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme