MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

MECECE ILLAR AURAN MATAR DA TA GIRMI MUJIN TA

Matasan Arewa na da wata al’ada ta tsangamar matashin da ya auri matar da ta fi shi shekaru, ba don komai ba sai don suna ganin ba zai samu yadda yake so a matsayinsa na maigida wanda akalar auren ke hannunsa ba.

Al’adar ba ta tsaya kan Hausawa ba kawai ta game har sauran kabilun da ke yankin Arewa, wadanda suke ganin al’adar ’yan Arewa ce ya zama miji ya girmi matarsa, wanda a ganina don mutum ya auri wacce ta girme shi ba wani aibu ba ne, idan da soyayya da kauna da aminci a tsakaninsu. Shi ya sa a kudanci ba wani abu ba ne don mutum ya auri wacce ta fi shi shekaru.
A wadansu wuraren ma har suna ake sanya wa mutumin da yake soyayya ko kuma ya auri wacce ta girme shi. Sai ka ji ana kiransa mijin tsohuwa ko a rika ce masa ya auri babarsa. Tun ba ma a ce bazawara ce wacce take da shekaru da yawa ba, kuma ta dauki shekaru da dama rabon ta da aure, ai sai ka ji ana ta yin maganganu da yawa a kan ta.
A ganina abin da ake bukata a aure shi ne tsayayya da kauna. Idan har matar da za ka aura tana sonka to babu shakka ka samu abin da ake bukata. Yawa ko karancin shekarunta ko ba shi da wani muhimmanci mai yawa.
Hasali ma abin da samarin yanzu ba su gane ba shi ne bazawara mai yawan shekaru wacce ta goge da rayuwa ta fi budurwa mai karancin shekaru dadin zama. Kuma ta fi ta sanin soyayya da yadda ake yin ta, sannan kuma ta fi ta iya abubuwa da dama na zamantakewar aure saboda ta yi aure ta ga yadda yake.
Dadin dadawa, idan ma matar ba ta taba aure ba mudddin tana da yawan shekaru za ka ga ta fi wacce ba ta da yawan shekaru fahimtar rayuwa. Domin yawan shekarunta zai sanya ta ga abubuwa da yawa na rayuwa wacce wadda take da karancin shekaru ba ta gani ba.
Mata masu karancin shekaru na wannan zamani sun rasa abubuwa da yawa. In dai ba ka yi sa’a ba da ka auri yarinya mai karancin shekaru in ba ka kai zuciya nesa ba kafin wata guda sai ka sake ta, saboda irin katobarar da za ta rika yi maka da kuma yarintar da za ta rika nuna maka musamman wajen dafa abinci da kwanciyar aure da sanin abin da kake bukata. Sai dai idan ka yi sa’ar gaske kamar yadda na yi, to shi ne za ka samu mace mai karancin shekarun da za ta rika yi maka abin da kake so ba tare da wata matsala ba.
Wani abokina ya taba shiga cikin tsaka-mai-wuya lokacin da ya yi yunkurin auren wata budurwa wacce ta dade ba ta samu miji ba, kuma ga shi ta fi shi yawan shekaru. Har sai da ta kai ’yan uwansa da mahaifiyarsa suka nuna bacin ransu a gare shi. Haka ma ya taba faruwa da wani wanda ya ya yi yunkurin auren wata bazarawa da ta fi shi yawan shekaru.
Wani matashi ya taba auren wata tsohuwa da ta yi jika da shi a Arewacin Najeriya. Mutane suka rika gutsuri-tsoma dangane da aure. A ganina bai yi kuskure ba domin a wajen ta ya ga soyayyar da yake nema shi ma da kansa ya fada cewa ta fi nuna masa soyayya a kan ’yan matan da yake nema.
Shi aure ba wani abu ba ne illa so da kauna da amince da kuma zaman lafiya. Saboda haka idan mutum ya samu macen da take da abubuwa da ake bukata komai yawan shekarun ta ni ban ga wata illa ba.

(Visited 1 times, 1 visits today)
Updated: 2017-07-20 — 2:00 pm

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme