MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

MA’AURATA: TSOTSAR AL’AURA A LOKACIN JIMA’I YANADA MATUKAR ILLA GA LAFIYAR JIKI-Inji Wani Likita

Wani Shaihun malami, Farfesa Adegboyega Fawole na asibitin koyarwa na jami’ar Ilorin, UITH ya gargadi al’umma da su guji dabi’ar nan na tsotsar al’aura a yayin jima’i, abinda Farfesan ya ce ya haddasa samuwar wata cuta mai suna Human Papiloma virus (HPV) a makoshin mutane jinsin maza da mata da dama

Farfesa Fawole wanda kwararre ne a bangaren a bangaren mata da yara da aturance a ke kira da Gynaecology, ya bayyana kamfanin dillancin labarai jiya a Ilorin cewa cutar HPV cuta ce da ake daukarta ta hanyar jima’i

Kwayar cutar ta bayiros na haddasa nau’o’in cutar daji da dama da ya hada da cutar dajin dubura, da ta al’aura da dai sauransu

Duk da cewa cutar ta HPV cuta ce da za a iya daukarta ta hanyar yin jima’i da wanda ke dauke da kwayar cutar, amma ana kamuwa da cutar sosai ta hanyar tsotsar al’aura a yayin saduwa

A saboda haka ne ma Farfesa Fawole ya ke jan hankalin masu aikata wannan dabi’ar da cewa, yiwuwar kamuwarsu da cutar HPV yafi yawa sama da wadanda ba sa wannan ta’ada

Sai dai Farfesa ya kara da cewa babu laifi ga lafiyayyun mace da mijinta da suka tsaya kawai akan junansu su gabatar da tsotse-tsotsen tunda babu wata barazana ta kasancewar akwai wani ko wata a tsakani da zai iya yada cutar a tsakaninsu

Farfesan ya yi kira ga ma’aurata da su ke zuwa bincikar lafiyarsu daga lokaci zuwa lokaci don tabbatar da lafiayarsu da ta abokan zamansu

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Shafin Facebook
Shafin Twitter
Shafin Instagram
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: [email protected]

Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa


Shiga Mujallarmu YouTube channel kayi subscribe domin kallon bidiyo da muka tanadar maka don nishadi da ilimantarwa
Updated: 2017-09-06 — 5:20 pm

1 Comment

Add a Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme