MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

KARANTA KAJI:MATAKAN AURE A AL’ADAR MALAM BAHAUSHE

  Al’ada: Matakan aure a Kasar Malam Bahaushe

Hausa na cikin manyan harsunan Najeriya da ma Afrika musamman ta yamma.

Kuma harkar a aure a wajen Malam Bahaushe kan burge wasu al’adun musamman yadda Addinin Musulunci yayi kane-kane a ciki.

Haka ya sa auren diyar Bahaushe ya fi araha kan auren wasu Kabilun a Najeriya.

Ka iya cewa matakan aure a Kasar Hausa guda 6 ne:

Wata Amarya a Ranar auren ta

1. Na gani ina-so Watau matakin farko kenan da zarar saurayi ya ga tsaleliyar Budurwar da yake so.

Daga nan sai ya nemi amincewar iyaye domin jarraba sa’ar sa. A nan ne ake fara binciken addini da nasaba da kuma dabi’ar juna.

2. Soyayya Daga nan idan an dace sai ka ga an fara kulla alaka har ta kai ga soyayya ana kara kuma fahimtar juna,idan abu ya gyaru sai ka ji an kai ga tambaya.

Hoton Amarya tasha kunshi.

3. Kayan Gaisuwa Bayan an yi zance iya zance sai dangin namiji su fara kai gaisuwa wajen dangin matar ana mika kayan gaisuwa irin su tufafi da kudi wanda da zarar an karba sai a fara maganar sadaki kuma.

4. Sadaki A addinin Musulunci yawanci sadakin diya mace ba ya kasa da rubu’i na dinari watau daya cikin hudu na farashin kilo na gwal. Idan akwai wadata kuma iya kudin ka iya shagalinka! Amarya ta sha kwalliya domin bikin aure

5. Sa rana Da ance an amince da kudin sadaki sai kuma a sa ranar daura aure. Saurayi zai nemi gidan da za a tare yayin da dangin mace ke kawata gidan.

6. Daurin aure da walima Shi kenan kuma sai Allah ya kawo ranar daurin aure inda Amarya za ta ci kunshi da duk wata kwalliyar Duniya shi kuma Miji ko wakilin sa a daura masa aure da matar sa.

Bayan nan sai ayi addu’o’in da za ayi da kuma ‘yar bikin walima domin a ci kuma a sha.

A karshe sai a kai amarya gidan mijin ta!

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Shafin Facebook
Shafin Twitter
Shafin Instagram
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: [email protected]

Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa


Shiga Mujallarmu YouTube channel kayi subscribe domin kallon bidiyo da muka tanadar maka don nishadi da ilimantarwa
Updated: 2017-09-10 — 8:24 pm

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme