MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

HADARIN ZAMA DA MACE DAYA!!!

Baffa Baba

Na san mata da kuma ragwayen maza za su yi

min ca akan wannan gaskiyar da zan bayyana,

amma dai ko ba komai na fadi hakika, na fadi

gaskiya, na amayar da abinda wasu suka kasa.

Zama da mace daya yana kawo illoli da dama ga

magidanci da su mata kansu da kuma al`umma.

 

GA MAGIDANCI :-

Yana rage masa nishadin aure.

Yana kawo tsufa da wuri.

Yana saka maigida cikin damuwa musamman a

kwanakin al`adar matarsa ko lokacin rashin

lafiyarta, ko idan ta yi tafiya.

Yana saka wa mace ta rika daga masa kai, tayi

masa yadda taso saboda ta san ba shi da yadda

zai yi.

Yana rage masa samun soyaiya da tarairaya da

kulawa da ya cancanta a matsayinsa na maigida.

Yakan hana shi tantance son na gaskiya daga

bangaren matarsa ko wanin haka.

 

GA SU MATA :-

Yana hana wadansu samun mazajen aure.

Yana dora wa matargida aiyukan da suka shige

misali kamar, kulawa da maigida, yarangida da ita

ma kanta.

Yakan hana mace samun isasshen hutu da

kuma lokacin kulawa da kanta.

Yana rage wa mace kuzarin nuna soyaiya ga

maigidanta.

Yana saka matargida cikin tsoro da fargaba

marasa yankewa.

Yana haifar da rashin amincewarta ga

maigidanta

da dauwamar da tuhuma ta har abada.

Yana saka mace cikin shirin yaki da dawainiyar

dakon makamai marasa ranar yankewa.

Yana saka mata yawan zargi ga dukkan matan

da suke da alaka da maigidanta ko ma wace iri

ce.

Yana kara mata zafin kishi da rashin nutsuwa

marasa ranar yankewa.

 

GA AL`UMMA :-

Yana haifar da karuwai mata marasa aure.

Yana bunkasa yawan zawarawa acikin

al`umma.

Yana dorawa al`umma karin nauyin kulawa da

mata iyayen marayu da marayun kansu.

Yana bunkasa zinace-zinace a cikin al`umma.

Yana rage tausayi da son bada taimako da

agaji daga zukatan al`umma.

Yana kara saka fargaba da tsoro a zukatan

iyaye wadanda suke da `ya`ya mata a gaba.

Yana bunkasa kasuwar malaman tsibbu da

bokaye.

 

WADAN NAN SU NE KADAN DAGA ILLOLIN

ZAMA DA MATA DAIDAI, DA FATAN MAGIDANTA

ZA SU GANE, MATA ZA SU TAIMAKAWA

JUNANSU.

Danna nan idan kana neman BIDIYON HAUSA masu ilimantar wa da NIshadantarwa musamman na Zamantakewa tsaknin Ma'aurata:


Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa

Updated: 2017-10-14 — 5:59 am

4 Comments

Add a Comment
  1. aliyu shehu abubakar

    Wannan Gaskiya ne kuma keda bakison amiki kishiya Idan Allah yabaki yaya Mata kuma mazajen gari sukace bazasu karaba yaya zakiyi dasu.

  2. Gaskiya ne

  3. Abubakar Abba Toyawa

    Na yarda da wadannan illolin da marubuci ya zayyana kashi 85%, abin daya sa bazan bashi 95% ba, saboda ya manta da wasu wadanda bai fada ba. Amma duk da haka LABA’ASA…. JAMILAN-JIDDAN…

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme