MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

LABARIN SOYAYYAR GASKIYA RIGA CE KASHI NA 1

Kausar da Aliyu sun fara soyayya ne
alokacin da suka hadu a wani bikin
aure da aka gayyaci kowane acikin
su.

AMINA AMAL TA BAYYANA ALAKAK TA DA ADAM ZANGO-
Sai dai kuma Aliyu ya kasance ya
fito daga zuri’ar talakawa ne inda ita
kuma Kausar ta kasance diyar wani
attajirin hamshakin mai kudi dan
kasuwa.

Kwanaki kadan da haduwar kausar
da Aliyu soyayya mai karfi ta shiga
zukatan su,inda har suka yiwa juna
alkawarin cewa inda rai da lafiya
babu abinda zai iya hana su auren
juna.

Aliyu ya kasance jami’in soja mai
kwazo a wajen aiki sannan ya
kasance dan soyayya tun a
makaranta,inda dama wasu abokan
sa suna yi masa da lakabi da
Sharukhan sarkin soyayya.
Sai dai kuma kash ba’anan gizo ke
sakar ba domin kuwa mahaifin
Kausar mutum ne mai tsattsauran
ra’ayi sannan da nuna kyama akan
talaka,inda kuma a wani gefe daban mahaifin kausar yafi son ‘yar sa ta
aure dan kasuwa wanda akoda
yaushe zai iya bata kulawa da nuna
soyayayr sa gare ta bawai soja ba
da baida lokacin kansa bare ace na
matar sa.
Watanni kadan da faruwar soyayyar
Kausar da Aliyu mahaifin ta ya samu
cikakken bayani game da
Aliyu,musamman akan aikin sa na
soja mahaifin kausar nan take ya
fara kumfar baki yana sambatu yana
cewa wallahi shi ‘yar sa bazata aure
soja ba.
Kasancewar Aliyu soja hakan bai
cire masa tausayi ba kamar yadda
mutane ke tunanin cewa wani sa’ilin sojoji basu da imani sosai,bayan
haka Aliyu ba kowa zai ya iya gane
cewa shi soja ne ba saboda kwata
kwata baya daukar kansa matsayin
soja yana gudunar da rayuwar sa
tamkar irin ta kowa.
Watarana Aliyu yaje hira wajen
kausar da yamma suna zaune acikin
farfajiyar cikin gidan su kausar,inda
ita kuma mahaifiyar kausar tayi
matukar farinciki sosai aranta
kasancewar yadda taga Aliyu ya
sanya farinciki acikin zuciyar ‘Yar ta
cilo,sannna har a zuciyar ta ta
gamsu da soyayyar da Aliyu yake
yiwa kausar cewa soyayya ce ta
gaskiya dake cike da amana.

Wasu awoyi kadan da zuwan Aliyu
gidan su Kausar sai mahaifin
Kausar Alhaji Sae’eed ya
dawo,shiga cikin gidan keda wuya
bayan mai gadi ya bude masa kofa
sai ya tsinkayi Aliyu da Kausar suna
hira a wani bangare na musamman
acikin gidan.
Alhaji Sae’eed ya samu yayi parking
na motar sa ya bude kofa ya
fito,amma sai dai ransa a bace ya
turnuke fuska tamkar wanda yaga
sabon kashi a hanya,wanna bacin
rai da Alhaji Sae’eed ke nunawa ba
akan kowa bane sai akan Aliyu
saboda kawai ya fito daga gidan
talakawa.

Aliyu da Kausar suna zaune suna
shan soyayyar su sai Kausar tace
da Aliyu Angona na gobe ga
sirikinka nan ya dawo wato
mahaifina saboda haka kazo muje
ka gaisa dashi a karon farko ,Aliyu
bai yiwa masoyiyar tasa gardama ba
cikin raha da shaukin so ya amsa
mata toh Amarya ta gobe muje din.
Kafin isowar su Aliyu da Kausar
wajen da ake parking din motocin
gidan mahaifiyar Kausar Hajiya
Saratu ta fito tayiwa Alhaji Sae’eed
barka da zuwa,bayan Hajiya Saratu
tayiwa Abban Kausar sannu da
zuwa kalmar farko data fito bakin
Alhaji Sae’eed itace,Hajiya waye? Ya bari wannan yaron ya shigo har
cikin farfajiyar gidana kuma yake
hira da ‘Yar cikina Kausar.
Hajiya Saratu tayi ajiyar zuciya
sannan tare da bayyana wani
matashin murmushi a fuskar ta tace
da Alhaji Sae’eed nice amma kayi
hakuri na manta na fada maka cewa
wannan shine sirikin mune na gobe
idan Allah ya yarda,saboda Kausar
tace ita shine zabin zuciyarta,abisa
wannan dalilin yasa nayi masa iso
daya shigo cikin gida.
Bayan hajiya saratu ta takai aya,su
kuma su Aliyu da kausar sun iso
wajen da Hajiya Da Alhaji suke a
tsaye,Kausar tace abba barka da dawowa sannan haka shima Aliyu
ya gaida mahaifin kausar Alhaji
Sae’eed cikin ladabi da biyyayya
tamkar yadda yake girmama
mahaifin sa.
Alhaji Sae’eed ya amsa sannan ya
dan saki fuskar sa kadan saboda
kada matar sa Hajiya Saratu da ‘yar
sa Kausar su fahimci wani abu
dalilin haka yasa ya danne komai
azuciyar sa amma ta ciki na ciki
,inda akarshe su duka suka tattaro a
waje daya suka ci abinci tare da
mahaifan Kausar da shi Aliyu.
Bayan sun kammala cin abinci a dai
dai lokacin da Aliyu yake ganin
lokaci yayi daya kamata ace ya tafi gida,sai dai kuma aransa yana san
ya shaidawa Kausar cewa gobe da
yamma zai tafi kasar Kamaru wajen
aikin soja sannan zai share shekara
daya kafin ya dawo,amma kuma
saboda son da yake yiwa Kausar
bayan san yaga abinda zaisa ranta a
damuwa gashi kuma maganar ta
zama dole sai ya furta.
Aliyu yayi shiru ya daina magana sai
sake sake yake a zuciyar sa yana
tunanin yadda zai bullowa al’amarin,
sai kawai mahaifiyar Kausar Hajiya
Saratu ta fahimci cewa kamar akwai
abinda Aliyu ke san furta,ai kuwa
nan take tace da Aliyu.

Domin Kallon Sababbin fina finan Hausa Cikin sauka sai kuyi downloading App na Mujallarmu Tv a nan:
Download Mujallarmu TV (284 downloads)

Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa


Shiga Mujallarmu YouTube channel kayi subscribe domin kallon bidiyo da muka tanadar maka don nishadi da ilimantarwa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme