Yadda ake kamuwa da cutar Monkeypox da hanyoyin kariya daga gare ta

Cutar Monkey Pox cuta ce da masana a fannin kiwon lafiya suka bayyana ta da cewa cuta ce mai matukar hatsari ga rayayyu. Cutar ana samunta ne daga dabbobi, irin su Birrai, Kyanwa, Bera, da sauran dangogin su.

Monkey pox kwayar cutar “Vaccinia virus” ce mai dangi da “OrthodoxVirus” wacce aka fara samun ta a yankin Copenhagen na kasar Denmark a shekarar 1958. An fara gano cutar daga jikin biri karon farko, inda aka samu korafai sama da 400 na cutar wacce daga nan ne cutar ta yadu zuwa ga dumbin mutane, wanda a shekarar 2003 an samu bayyanar cutar a kasar Gambia.

A watan da ya gabatan nan ne aka samu bayyanar cutar a jihar Bayelsa na yankin Niger-Delta na Najeriya. An bayyana cutar, da cuta ce mai alamomi irin na cutar cin zanzana wato small pox.

Hanyoyin kamuwa da cutar

Kamar yadda masana suka tabbatar ana kamuwa da cutar ta hanyar cin duk wata dabbar da ke dauke da cutar, haka kuma ana iya kamuwa da cutar ta hanyar yin mu’amala da mutumin da ke dauke da cutar, muddin aka samu alaka na hada jiki ko musanyar kayan sawa, ko yin fitsari ko kashi waje daya da mai dauke da cutar.

Su wa suka fi kamuwa da cutar?

Ciwon yana iya kama kowa babba ko yaro, tsoho ko matashi, mace ko namiji, mai ciki ko marar shi.

Yaushe alamomin cutar ke fara bayyana?

Masana a fanin kiwon lafiya sun bayyana cewa, cikin kwanaki bakwai zuwa sha hudu alamomin ciwon kan fara bayyana a jikin mutun da zarar ya kamu da cutar, wani lokacin kuma daga kwana 5 zuwa 21 alamomin kan bayyana. Alamomin cutar sunhada da:

1. Zazzabi

2. Jin sanyi ko mutum ya rika tsuma.

3. Fama da zufa musamman da daddare in ana bacci.

4. Ciwon kai

5. Jin ciwo cikin naman jiki

6. Ciwon baya

7. Kurajen jiki masu masifar kaikayi

8. Yawan jin bacci da kasala

9. Fitowar kaluluwa abangarori daban-daban na jiki

Matakan Kariya daga cutar kuma sun hada da:

1. Tsafta (wanke hannu): a koda yaushe mutane su zamto suna tsaftace hannuwansu da sabulu kafin cin abinci da bayan cin.

2. A kiyayi cin dabbobi marasa lafiya na gida ko na jeji.

3. A kiyayi cin matattun dabbobi.

4. Ayi hanzarin kebe duk wanda alamomin cutar ta fara bayyana a jikin shi kuma a hanzarta sanar da jami’an kiwon lafiya.

5. Ga jami’an kiwon lafiya, a rinka amfani da kayan kariya wato (personal protective equipment), irin su hand gloves, lab coat, da duk wani nau’in abinda zai bada kariya yayin kula da mai dauke da cutar.

Maganin cutar

Zuwa Yanzu babu wani takamammen magani ko allurar rigakafin cutar da aka tabbatar. Sai dai ana kokarin dakile annobar ta hanyar amfani da ruwan maganin smallpox (small pox vaccine) a duk san da aka sami bullar cutar kuma ana samun nasara kaso 85% idan a kayi hakan.

Adams Garbage

Shafin Bakandamiya

This website uses cookies.