MAHIMMIN SAKO GAME DA LARURAR CIWON SUGA

Ciwon suga larura ce da ke bukatar kulawa da jiki ta waje baya ga maganin da ake sha.

Dukkan masu ciwon suga suna cikin hatsarin samun rauni a tafin kafarsu kaso 60% cikin dari mussamman mutane masu kiba, Saboda yawan kitse (cholesterol) dake cikin jijiyoyin jininsu na rage karfin tafiyar jinin zuwa sassa daban daban na jiki mussamman kafafuwansu wanda wannan shikesa ake samun neuropathies wato nerve damages.

1- Jin zafi a tafin kafa kamar an taka simintin da ya dau rana,

2- Jin zafi kamar an tsiri mutum da allura a atafin kafa,

3- Jin kafa tayi dundurus kamar ba ajikin mutum take ba koda an tsireta baiji sosai,

4- Da kuma jin zafi kamar an yanki mutum a kafa.

Wadannan alamun na sama duk warning sign ne na gargadi game da diabetes dake nuni da fara lalacewar jijiyoyin jinin kafa wanda hakan kesa asami poor blood flow yayin da da zarar aka ji ciwo a kafa Tôfã sai kiyayewar Allah domin abune mai sauki ace sai ankai ga yanke kafar.

DON HAKA

▶ Yawan jin yunwa.

▶ Yawan jin kishirwa

▶ Rama cikin kankanin lokaci.

▶ Yawan fitsari

▶ Yawan kasala

▶ Gani dusu-dusu

▶ Rashin kuzari yayin jima’i

▶ Ciwon sanyi gaban da yaki ci yaki cinyewa (vaginal infection)

Duk Alamomin ciwon suga ne.

SHAWARA

A tafi asibiti ai gwaji koda bakajin wannan alamun kaje kace aima (RBS ko FBS) Test domin kasan matsayinka.

Normal sugar level ya fara daga 3.7 mmmol zuwa 6.9mmol duk abunda ya haura yaje 7.0mmol  zuwa 8.9mmol wannan are pre- diabetics xuwa diabetes Suna bukatar dauki da shawarwari don haka kuskurene da jahilci duk ilimin ka ko matukar kace waikai bazakaje awo ba kada a fadama abunda zai hanaka bacci.

Kasani inbakaje anfada ma abunde yana nan ajikinka, mutuwa munsan kowa zatazo kansa Amma wahala da doguwar jinya sune abunda bama fata don haka shawara ce ga dukkan wanda ya karanta post din nan ban daukemai ba, har jami’an lfy Akan samu masu irin wannan tunanin na banza don haka kuje kusan matsayinku.

Sannan ga wadanda suka san suna da wannan matsala akoda yaushe kuke yawan zama kuna duba tafukan kafarku zuwa tsakanin yatsun ku ku tabbatar ba rauni ba kurji, ku guji sanya safa da takalmi mai rufi sosai yayin da ya zamto akwai damshin lema a kafar.

Ku guji sanya takalma masu tsini, wannan ba naku bane.

Ga Yan uwana kuje kui gwaji, wannan ciwon yafi mana illah domin sai ya gama damu ake ganosa Saboda bama zuwa gwaji su mata yawanci wajan awon juna biyu ana ganomusu shi abasu magani mukam muna da taurin kai ko rashin lfy maza sunfi zuwa chemist Akan asibiti. Don haka mu kula mu farka.

Allah ya dada karemu Amin👏👏

IN KUNNE YAJI……………!

(Ibrahim Y. Yusuf)

This website uses cookies.