MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

KARANTA KAJI: KALAR ABINCI UKU DAKE HAIFAR DA WARIN BAKI AKODA YAUSHE

           KARANTA KAJI KALAR ABINCI UKU DAKE HAIFAR DAWARIN BAKI AKODA YAUSHE

Marubuci;Haruna Sp Dansadau

Kamar yadda Mujallarmu tayi nazari a wannan karo tayi kokarin kawo muku wasu kalolin abinci dake matukar haifar da warin baki ga mutum.

Hakika warin wani abune dake da matukar illar da kunyata mutum acikin abokan sa ko matar sa,sannan wani lokaci ya kan haifar da illoli masu yawa ga lafiya jiki.

Sai dai kuma Dandalin Mujallarmu ta kawo sunayen abinci dake haifar da warin baki,don ganin mutane sun kaurace masu.

  • MADARA

Nasan da dama mutane zasu mamakin cewa ya akayi sunan madara ya fito farko acikin jerin sunayen abinci mai sanya warin baki,toh ku gafarce mu hakikanin gaskiya madara tana dauke da wani sinadri maisuna Amino acid wanda zai iya haifar da warin baki a kowane lokaci,zaka iya shan madara iya yadda kake so amma ka wanke bakin da zarar ka kammala sha.

Wannan itace kadai hanyar da zaka iya magance warin baki.

 

  • ALBASA DA TAFARNUWA

Albasa da tafarnuwa suna da matukar sanya abinci yayi dadi sosai,sannan yanzu zan iya cewa mafi yawan akasarin mata suna amfani dasu sosai wajen girki,toh sai dai mai gida yakamata ka lura a yayin da kagama cin abinci ya zama baka wajibi ka wanke bakin idan kana son ka kauracewa warin baki.

  • SHAYIN COFFEE

Shayi na daya daga cikin abinci hudu dake sanya warin baki,duk da cewa shi ya kasance abin sha ne,saboda haka yazama wajibi gareka ka lura bayan kagama sha,kayi kokari tsaftace bakinka.

 

Danna nan idan kana neman BIDIYON HAUSA masu ilimantar wa da NIshadantarwa musamman na Zamantakewa tsaknin Ma'aurata:


Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa

Updated: 2018-08-01 — 6:59 pm

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme