MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

KARANTA KAJI: AMFANIN RIDI 10 A JIKIN DAN ADAM

                                   Amfanin ridi guda 10 a jikin Dan Adam

Al’umman kasar Najeriya na noman ridi sosai sannan kuma mutane na sarrafa tare da amfani da shi wajen yin abubuwa da dama musamman wajen yin abinci da sauran su,da dama na da masaniya game da ridi sai dai yadda suke amfani da ita ne ya banbanta.

Ana amfani da ridi wajen ci haka kawai da siga ko kuma da gishiri. Wasu kan hada shi don maganin bakon dauro a yara sannan kuma wasu kan markada sannan su cire man shi don amfani da shi a abinci, man kai da na jiki da dai sauransu.

Likitoci sun yi kira ga mutane da su rika cin ridi don amfanin da yake da shi a jikin mutum

Ga wasu daga cikin amfanin ridin:

1. Ridi na rage cutar siga.

2. Ridi na taimaka wa masu fama da ciwon ido.

3. Ridi na taimakawa wajen nika abinci a cikin mutum.

4. Yana rage kiba a jiki.

5. Yana kuma kawar da cututtukan dake kama zuciya.

6. Ridi na maganin Asma.

7. Ridi na dauke da sinadarin Iron dake taimakawa wajen kawar da cututtukan dake kama jini.

8. Yana dauke sinadarin Folic Acid dake taimakawa mata masu ciki da dan dake cikin su.

9. Ridi na karfafa karfin kashi.

10. Yana kawar da cututtukan dake kama fata kamar su kuraje kuma yana hana tsufa da wuri.

Danna nan idan kana neman BIDIYON HAUSA masu ilimantar wa da NIshadantarwa musamman na Zamantakewa tsaknin Ma'aurata:


Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa

Updated: 2019-01-24 — 10:34 am

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme