MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

KARANTA KAJI: Amfanin Danyen Tumatir 4 A Jikin Dan Adam Da Watakila Baku Sani Ba

          Lafiya uwar jiki: Anfanin tumatir a jikin dan adam da watakila baku sani ba

Tumaturi dai wani dan icce ne ko kuma daya da cikin kayayyakin marmari kamar yadda wasu kan ce da ke kunshe da kusa kaso 95 cikin dari na ruwa da kuma sinadaren karin karfi da kuma na saukaka sarrafa abinci a sauran kaso 5 din cikin dari. Wasu kan ci tumatur danyen sa wasu kuwa sai an dafa, wasu kan ci shi shi kadai wasu kuwa idan an hada shi da sauran ganyayyaki da itacen itatuwa saboda alfanun sa.

Majiyar mu ta samu cewa tumatur yana da matukar anfani a jikin dan adam kuma ba kowa ne ya gane hakan ba shi yasa ma muka zayyano maku su nan a kasa:

1. Yana saukaka nakar da abinci Tumatur yana dauke da sinadaran dake kara saukaka narkar da abinci da sauran cima. Idan mutum na fuskantar matsalar narkar da abinci to tumatur zai yi masa anfani sosai.

2. Yana kara karfin ido Tumatur yana kunshe da sinadarin lycopene, lutein da kuma beta-carotene wadanda dukkan su suna taimakawa wajen kara karfin ido da gani.

3. Yana taimakawa wajen gyaran jiki da fata

4. Tumatur yana dauke da sinadiran da ke daidaita adadin suga

 

Danna nan idan kana neman BIDIYON HAUSA masu ilimantar wa da NIshadantarwa musamman na Zamantakewa tsaknin Ma'aurata:


Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa

Updated: 2019-01-12 — 12:20 pm

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme