MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

KARANTA KAJI: AMFANIN ABARBA 13 A JIKIN DAN ADAM

      Lafiya uwar jiki: Amfanin abarba 13 a jikin dan adam

Musamman ma kare jiki daga kamuwa da ciwon zuciya. Abarba na daya daga cikin yayan itatuwa masu amfani a jikin dan adam.
Abarba na da matukar amfani a jikin dan adam saboda tana dauke da muhimman abubuwa; fibres, menirals, vitamins, Nutrient da kuma Anti Oxidant.
Wadannan sinadarai dai dake a cikin abarbar na da matukar amfani ga rayuwar dan adam, sannan takan kare jiki daga cututtuka.
Dandalin Mujallarmu.com da ta zakulo maku kadan daga amfanin Abarba:
1. Tana dauke da sinadarin magnees da calcium wanda ke kara karfin kashi
2. Tana dauke da anti oxidant wanda ke kara ma jiki lafiya da kare jiki daga saurin tsufa.
3. Tana maganin mura da sanyin kirji.
5. Tana kara ma garkuwar jiki lafiya da kare shi daga cututtuka.
6. Tana maganin kamuwa da ciwon zuciya ta hanyar rage cholesterol a jiki.
7. Tana kara lafiyar dasashi da kare hakora.
8. Tana saukaka yawan laulayin ciki, da yawan amai da yawan tashin zuciya.
10. Tana maganin tsutsar ciki.
11. Tana kara ma idanu lafiya
12. Tana kara lafiyar ciki da saukaka bahaya
13. Tana maganin kumburi da maganin ciwon ga babuwa da fatan zamu rinka shan abarba akai akai.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Shafin Facebook
Shafin Twitter
Shafin Instagram
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: [email protected]

Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa


Shiga Mujallarmu YouTube channel kayi subscribe domin kallon bidiyo da muka tanadar maka don nishadi da ilimantarwa
Updated: 2017-09-16 — 5:21 pm

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme