GWAMNATIN JIHAR KADUNA ZATA  DAUKI MA’AIKATAN KIWON LAFIYA 1,000

Gwamnatin jihar Kaduna tace zata dauki ma’aikatan kiwon lafiya sama da 1000 don bunkasa harkar lafiya a jihar.

Kwamishinan lafiya na jihar Kaduna Dakta Paul Dogo ya bayyana hakan a taron tsakiyar shekara da ma’aikatar sa ta shirya da hadin gwiwar kafafen ‘yada labarai da kungiyoyi ma su zaman kansu dake jihar.

Ya ce, tuni gwamnati ta baiwa wasu makaikatan kiwon da ta dauka aiki su 418 takardun kama aiki kuma an fara tura su inda zasu gudanar da ayyukan su.

Acewar kwamishinan, sauran daukar aikin, Hukumar Ma’aikata ta jihar zata gudanar dasu.

Yacen waxanda za a dauka aikin sun hada da Likitoci 100 da Nas 1000 da masu kula da harkar magunguna 25 30 da kwararru 10 da likitocin qashi 20 da masu kula da vangaren abinci mai gina jiki da kara lafiya.

Dogo ya ci gaba da cewa, sauran sun hada da daukar ma su ajiyar bayanan lafiya 10 staff, 10(radiographers) da kuma masu kula da matsalar haqora su 10.

Ya ce, za a tura ma’aikatan zuwa Asibiti da matakan lafiya kanana da sauran cibiyoyin lafiya dake fadin jihar.

In za a iya tunawa, gwamnatin a wani taro a watan Janairu ta wannan shekar ta bayyana cewar zata dauki ma’aikatan lafiya har 1,245 don shawo kan matsalar mutuwar mata masu juna biyu a jihar.

Kwamishinan ya kuma bayyana cewar gwamnatin ta ta kirkiro da wani shiri na lafiya don zata gudanar dashi kyauta don taimakawa tsofaffi ma su fama da hawan jini da ciwon Suga.

Dogo ya ce tsofaffi ma su shekaru 70 zuwa sama zasu amfana da shirin, da kuma marasa karfi dake jihar.

Ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta shirin yin hadin gwiwa da wani babban kamfanin magunguna da zata baiwa naira 200, 000 duk shekar don don yiwa tsofaffi rijista a Asibitocin dake jihar don duba lafiyar su.

Acewar shi, gwamnatin jihar ta horar da ma’aikatan kiwon lafiya su guda 200 don duba tsofaffi masu hawan jini da ciwon Suga.

Ana shi jawabin na maraba a wurin taron, Shugaban kungiyar bindiddigin yadda gwamnatuin take kashe kudi a fannin lafiya wato (KADMAM) Alh Mustapha Jumare,ya nuna damuwar sa akan yadda ake jinkiri wajen habaka kananan matakan guda 255 da ake dasu a jihar.

Jumare ya ce, a bisa binciken da kungiyar ta gudanar ta gano cewar a karshen watan Satumba, ya nuna cewar, daga cikin matakan guda 255 da ake dasu a jihar, 11 ne kawai aka dauka ka matsayin su.

A wani bayani da aka samar daga ma’aikatar lafiya ta jihar, ya nuna cewar, gwamnatin jihar a yanzu tana kan dauka ka martabar matakan lafiya wadanda yawancin su ana gab da kammala aikin su.

A cikin watan Satumbar shekarar 2017, 11 daga cikin 255 na kanan cibiyoyin matakan lafiya na farko, an kamla aikin su.

Bayanan sun nuna cewar ma’aikatar lafiya ta jihar tana taimakwa gwamnatin jijar wajen yiwa kanan matakan lafiya na farko kwaskwarima da kuma dauka ka darajar guda 40 PHCs.

Kungiyar ta gudanar da binciken ne da nufin tabbatar da Kananan matakan lafiyar na farko na jihar, ko an dauka ka darajar su yadda ya kamata a bisa shawar da matakin lafiya na kasa ya bada shawara.

This website uses cookies.