MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

ZARGIN RASHAWA AN KAMA TSOHON SHUGABAN KASAR FARANSA NICOLAS SARKOZY

ZARGIN RASHAWA

AN KAMA TSOHON SHUGABAN KASAR FARANSA NICOLAS SARKOZY

Daga Auwal M Kura
29/03/2018

Jami’an Yan Sanda Kasar Faransa Sun Kama Tare Da Garkame Tsohon Shugaban Kasar Faransa, Nicolas Sarkozy, Kan Zargin Da Karbar Milyoyin Kudade Daga Gurin Tsohon Shugaban Kasar Libiya Muhammad Gaddafi, Ba Bisa Ka’ida Ba Wanda Yayi Amfani Dasu Gurin Yakin Neman Zabe.

Sarkozy Dan Kimanin Shekaru , 63, Wanda Shine Shugaban Kasar Ta Faransa Daga Shekarar 2007 Zuwa 2012,

Da Yake Amsa Tambayoyi A Ranar Talatar Nan Data Gabata A Ofishin Yan Sanda Dake Nanterre,dake Arewa Maso Gabashin Paris.
Sarkozy Ya Karyata Zargin Da Akeyi Masa Inda Yace Wannan Kage ne Da Yarfe Akeyi masa.

Sai Dai Jami’an Dake Binciken Sun Gano Yadda Gaddafi Ya Turawa Sarkozy euro Milyan Hamsin A Boye Domin Yakin Neman Zaben Sa Na 2007.

Wanda Hakan Ya Sabawa Dokar Amsar Kudi Daga Kasashen Waje Da Kuma Dokar Bayyana Hanyoyin Da Kasamu Kudin Yakin Neman Zabe Ta Kasar Faransa.

A Watan Afrilun Shekarar Dubu Biyu Da Sha Biyu 2012,An Binciko Wasu Bayanai Da Wata Jaridar Yanar Gizo Ta Saka Dake Nuna Tabbacin Amsar Euro Milyan Hamsin Wanda Aka Turawa Sarkozy Daga Libiya Domin Yakin Neman Zabe

Updated: 2018-03-29 — 1:42 am

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme