MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

ZAN BAWA ‘YAN LUWADI DA MADIGO CIKAKKEN ‘YANCI IDAN NAZAMA SHUGABAR KASA A NIJERIYA-Inji Oby Mace Yar Takarar Shugaban Kasa

Bazan Kyamaci ‘Yan Luwadi Da Madigo Ba A Gwamnatina Ba Idan Nazama Shugabar Kasa A Nijeriya-Inji Oby

Yar takarar shugabar kasar Nigeria karkashin jam’iyar ACPN, Obiageli Ezekwesili ta tabbatar da cewa gwamnatinta zata yi adalci ko kwanne irin mutum ba tare da duba dabi’arsa ba, wandanda suka hada da ‘yan luwadi da ‘yan madigo (LGBT). Ta bayyana hakan ne a lokacin da aka tambayeta, a wata tattaunawa da Bisi Alimi tayi da ita a kasar Landan, kan cewar ko zata sakarwa ‘yan madigo da ‘yan luwadi mara idan ta zama shugabar kasa.

Ta ce, “Idan har za a yi adalci ga kowa, to babu dalilin nuna tsangwama ga wasu bangare na mutan,ko kadan ba zan damu da yardar ka ba, ko wata hanya da ka zabi binta, kowa nada ra’ayinsa, kuma kowa na da ‘yancin bin wannan ra’ayin.

“Na yarda da tafiyar da mutane kan gaskiya da adalci, don haka al’umar LGBT zasu skata su wala a gwamnatina ba tare da wani shakku ba. Kuma rashin nuna kyama ga wani bangare na al’umma na daga cikin tsarin gwamnatina idan har na zama shugabar kasa.”

 

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Shafin Facebook
Shafin Twitter
Shafin Instagram
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: [email protected]

Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa


Shiga Mujallarmu YouTube channel kayi subscribe domin kallon bidiyo da muka tanadar maka don nishadi da ilimantarwa
Updated: 2018-12-06 — 1:41 am

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme