MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

ZAMUYI KACA-_KACA DA SAUDIYA CIKIN AWA 48 KACAL — IRAN

Zamuyi Kaca-Kaca Da Saudiya Cikin Awa 48 – Iran

DAGA AUWAL M KURA

Mai Baiwa shugaban rundunar soja Iran,Janar Redha Kharam Tussi ya ce kamata yayi Saudiyya ta daina tsokanar su,saboda sun tanadi karfin da zasu iya ganin bayan ta cikin yawanni 48

Tussi ya ce,”Ina yi wa shugabannin Saudiyya hannunka mai sanda game da tsokanar fitina da kuma furta kalaman wuce gona da iri.Baku da karfi da kuma isassun makaman da zaku yi tinkaho da su.Awanni 48 kacal sun ishe mu yin kaca-kaca da kasarku.Shi yasa ku rufe bakunanku ku zauna”..
Game da tunkunmai da kuma cuzgunawar da Amurka ke ci gaba da yi wa kasarsa,Janaran ya ce,kasar Iran ta kasance a wani muhimmin matsayi,wanda ke sauwaka ma ta yin fito-na-fito da daya daga cikin manyan makiyanta, Amurka.
Janar Tussi dai ya furta wadannan kalaman don mayar wa da yarima mai jiran gado na masarautar Saudiyya,Muhammad bin Salman da martani dangane da cin fuskar da yi musu a ranar 29 ga watan Maris na bana tare da cewa nan da shekaru 10 zuwa 15 kasarsa za ta fafata yaki da Iran.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Shafin Facebook
Shafin Twitter
Shafin Instagram
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: [email protected]

Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa


Shiga Mujallarmu YouTube channel kayi subscribe domin kallon bidiyo da muka tanadar maka don nishadi da ilimantarwa
Updated: 2018-04-22 — 12:41 pm

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme