ZABEN 2019 ZAMU RAKA BUHARI DAURA IDAN YA FADI – MINISTA SALAMON DALONG

Zamu Raka Buhari Daura A 2019 Idan Ya Fadi Zabe — Salamon Dalong

Daga Auwal M Kura

22/04/2018

Ministan Al’adu Da Wasanni Mista,Solomon Dalong Yace Matukar Shugaban Kasa Muhammad Buhari Baiyi Nasara A Zaben Da Zai Gudana Na Shekarar Dubu Biyu Da Sha Tara Ba Shida Sauran Yan Uwansa Ministoci Zasu Karbi Kayin Da ‘akayi Masa Sannan Su Rakashi Har Daura.

Darlong Ya Kara Da Cewa” Zamu Fadawa Buhari Yayi Hakuri Allah Ya Riga Da Ya Tsara Cewa Nan Ne Karshe Mulkinsa Nan Karshen Iyya Kokarin Da Zaiyi,

Darlong, Ya Bayyana Haka Ne A Wata Tattaunawa Da Yayi BBC A Kaduna , inda Ake Dashi Game Da Abubuwan Da Suke Gudana A Najeriya, Sai Dai Darlong Ya Bayyana Shugaban Kasa Buhari A Matsayin Dan Takara Daya Tilon Daya Cancanci Zarce A Zaben 2019.

Yayin Da Aka Tambayeshi Cewa Ko Yana Ganin Buhari Zai Lashe Zaben 2019, Darlong Yace” Ni Ba Allah Bane Don Haka Allah Ne Kadai Wanda Zai Lashe Zaben 2019. ya Kara Da Cewa Munanan Munajiran Muga Wanda Zai Fito Matukar Ya Kai Ingacin Buhari Idan Kuma Bai Kaiba Zamu Bashi Shawara Kada Ya Wahalar Da Kanshi

This website uses cookies.