MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

ZABEN 2019: YANA TSAKANIN BUHARI DA ATIKU-Inji Mr Femi Falana

A 2019 za’a zabi Buhari ko Atiku, muna cikin mawuyacin hali – in ji Femi Falana

Mr. Femi Falana (SAN) ya ce, yana baƙin ciki game da yiwuwar cewa zaben shekarar 2019 zai kasance tsakanin shugaba Buhari da Atiku Abubakar
Falana ya bukaci ‘yan Najeriya su kalubalanci shugabanin akan ci gaban kasar
Lauyan ya soke lamirin fastocin Najeriya, ya ce sun fi kowane fasto arziki a duniya Babban lauyan nan, mai kare hakkin bil adam, Mr. Femi Falana (SAN) ya ce, yana baƙin ciki game da yiwuwar cewa ‘yan Najeriya za su zabi shugaba Muhammadu Buhari ko kuma tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar a zaben shekarar 2019. Mista Falana ya bayyana haka yayin da yake magana a wani taron tattaunawa a Legas.
Ya bukaci ‘yan Najeriya su yi amfani da yanar gizo don tada al’amurra masu muhimmanci ga cin gaba da kuma makomar kasar.

 

Har ila yau, lauyan ya kuma caccaki gwamnan jiharsa watau gwamna Ayodele Fayose na jihar Ekiti wanda ya bayyana shi a matsayin’Trump’ na jihar.

Falana ya zargi shugabannin addinin Krista, inda ya ce, “Fastoci masu karfin arziki a duniya sun kasance daga Najeriya ne, amma duk da haka mutanenmu suna fama da talauci da kuma yunwa.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Shafin Facebook
Shafin Twitter
Shafin Instagram
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: [email protected]

Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa


Shiga Mujallarmu YouTube channel kayi subscribe domin kallon bidiyo da muka tanadar maka don nishadi da ilimantarwa
Updated: 2017-11-12 — 2:56 pm

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme