YAYIWA YAR’SA CIKI BAYAN YAYI MATA FYADE HAR SAU BIYU

Wani Mutum Yayiwa Yarshi Ciki Bayan Yayi Mata Fyade Har Sau Biyu A Jahar Gombe

Daga Auwal M Kura

Wani Mutum Mai Kimanin Shekaru 50 Mai Suna Sama’ila Zakari, Ya Dirka Yar’Shi Daya Haifa Mai Kimanin Shekaru 15 Ciki Bayan Yayi Mata Fyade Har Sau Biyu.

Wannan Al’amari Ya Auku Ne Wani A Kauyen Deba Dake Karamar Hukumar Yamalatu/Deba A Jahar Gombe, Inda Isma’ila Zakari Yake Tilastawa Yar Tashi Kwanciya Dashi A Duk Sanda Ta Shiga Dakinsa ,Wanda Yanzu Haka Yarinyar Tana Dauke Da Cikin Watanni Biyu,

Yanzu Haka Dai Tuni Rundunar Yan Sanda Jahar Gombe Ta Cika Hannu Dashi,Kana Kuma Ta Gurfanar Dashi A Gaban Kotu Domin Fuskantar Hukunci, Inda Mai Shari’a Mista Dorabo Sikam Ya Bada Umarnin Cigaba Da Tsareshi Har zuwa Ranar 21 Ga Watan Mayun Shekarar 2018 Da Muke Ciki Domin Cigaba Da Sauraron Karar.

This website uses cookies.