‘YAN SANDA SUN CAFKE WANI SAURAYI DAN SHEKARA 25 DA KOKON KAN MUTUM A HANYAR SA TA ZUWA GIDAN TSAFI-Karanta Kaji

‘Yan Sanda Sun Cafke Wani Saurayi Dauke Da Kokon Sabon Kan Mutum.

Marubuci:Haruna Sp Dansadau

Rahoton da muke samu yanzu daga babban ofishin jihar Ogun jami’an ‘yan sandan yankin sun cafke wani matashin saurayi mai kimanin 25 dauke da kokon sabon kan mutum a hanyar ta zuwa gidan tsafi.

Mai magana da yawun ‘yan sandan Mr Abimbola yace sunyi nasarar kama mutumin ne a bakin daji kusa da cikin garin na Ogun,inda yake kokarin kutsawa wani gida da ake kyautata zaton na masu tsafi da sassan mutum ne don suyi kudi.

Yanzu haka wannan matashi yana tsare a ofishin ‘yan sandan jihar ta Ogun ana cigaba da tuhumar sa.

This website uses cookies.