MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

Yadda matar talakan Najeriya ta fi matar gwamna morewa

Babu shakka matar gwamna na daga cikin matan da dubban mata ke sha’awar rayuwar su kuma suke fatan ina ma su ma su kai wannan matsayi.

To sai dai watakila idan wasu matan suka ji yadda matan gwamnonin ke rayuwa za su ga cewa ba komai ba ne ya ke da dadi a rayuwarsu.

Kowane dan adam dai yana bukatar sirri a rayuwarsa, domin samun damar yin walwala yadda ya ke so.

A bangarensu, wasu matan gwamnoni na cewa ba su da wannan sirrin a rayuwar su.

Mai dakin gwamnan jihar Kebbi Hajiya Aisha Bagudu ta ce daya daga abuwan da ke damunta a matsayin matar gwamna shi ne
rashin sirri.

Ta ce ko me ta ke yi ba ta da sirri, duk da cewa tana son shiga jama’a ba tare da ana yi mata wani kallon cewa wannan wata mata
ce ta daban ba.

Wani kalubalen kuma a cewarta shi ne, yadda zama matar gwamna ya ke zame mata kalubale wajen tafi da kungiyarta.

Ta ce a da jama’a suna bawa kungiyar gudunmuwa, kuma duk kokarin da aka yi mutane suna yabawa.

Amma ta ce a yanzu mutane sun daina bai wa kungiyar gudunmuwa, kuma ba a yabawa da yunkurin da suka yi, sabo da ana ganin ta
matar gwamna ce.

To amma Hajiya Aisha Bagudu ta ce
kungiyar ta ba ta gwamnati ba ce, kuma ba da kudin gwamnati ta ke tafiyar da ita ba.

Kungiyar dai tana tallafawa rayuwar
almajirai ne da mata marasa galihu.

Danna nan idan kana neman BIDIYON HAUSA masu ilimantar wa da NIshadantarwa musamman na Zamantakewa tsaknin Ma'aurata:


Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa

Updated: 2018-09-01 — 11:07 am

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme