WATA SABUWA: WASU GWAMNONI SUN FARA NEMAN SHAWARAR EL’RUFA’I KAN YADDA ZASU SHIRYA JARABAWAR GWAJI GA MALAMAN MAKARANTA-karanta Kaji

Gwamnonin jihohi zasu shirya jarabawar gwaji ga Malaman Makaranta

Dangane da batun gudanar da sahihin gyara a bangaren ilimi a jihohin kasar nan da ma kasar gabaki daya, wasu gwamnonin Najeriya sun shirya sa kafan wando daya da tabarbarewa Ilimi.

Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya bayyana a shafinsa na sadarwar zamani, Twitter cewa wasu gwamnonin Najeriya sun fara tuntubarsa, don sanin hanyoyi daya dace su bi wajen gudanar da jarabawar gwaji ga Malaman makarantun jihohinsu.

Kwamishinan Ilimin jihar Kogi yana amsan bayanai Dandalin Mujallarmu.com ta ruwaito Gwamnan yana fadin cewa gwamnatin jihar Kaduna zata cigaba da baiwa jihohin da suka nuna sha’awar gudanar da irin wannan jarabawa duk wasu bayanai da suka bukata, tare da basu goyon bayad don ganin an inganta fannin ilimi.

El-rufai ya bayyana haka ne yayin da kwamishinan Ilimi na jihar Kogi, J.S Tolorunleke ya kawo ziyara zuwa Kaduna don samun bayanan yadda aka shirya jarabawar a Kaduna, don su ma su shirya jarabawar a jihar su.

Shugaban mulki na hukumar Ilimi na bai daya, SUBEB, Alhaji Abubakar Salihu ne ya mika ma kwamishinan takardun dake kunshe da bayanai dangane da tsare tsaren jarabawar, inda shi ma kwamishinan ya yaba ma kokarin gwamnatin jihar Kaduna, karkashin Nasir El-Rufai.

This website uses cookies.