MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

WATA SABUWA: WANI MINISTAN SHUGABA YA SAYI GIDAN NAIRA MILIYAN N280 A ABUJA-Karanta Kaji

Tirkashi Wani Ministan Shugaba Buhari Ya Sayi Dankareren Gida Na Naira Miliyan N280 A Abuja.

Marubuci:Haruna Sp Dansadau

Ministan babban birnin tarayya Muhammad Bello ya sayi dankareren gida daya kai darajar kudi naira miliyan N280 a Abuja.

Ministan ya sayi gidan ne tun a shekarar data gabata 2017,sai dai kuma ba anan gizo ke sakar ba,don kuwa gwamnatin tarayya ta sanya ido ga dukkanin ministocin Najeriya ta hanyar lura da yadda suke batar da kudi ko sayen wasu manyan kadarori.

Kamar yadda majiyar ta Dandalin Mujallarmu,keda labari yanzu haka dai ministan yana fuskantar kalubale daga gwamnatin tarayya,inda gwamnati ta bukaci yayi mata cikakken bayanin inda ya samu kudin daya sayi wannan gida Miliyan N280 a Abuja.

Minista Muhammad Bello yace ya sayi gidan ne amatsayin bashi dazai rinka biya a hankali,sai dai kuma abisa bincike da akayi akan albashin da ministoci ke karba aduk karshen wata baida kudin da zai iya sayen gidan koda kuwa zai hada albashin sa na tsawon shekaru hudu da yayi akan kujerar minista.

A yanzu haka dai gidan yana karkashin kulawar jami’an gwamnati har sai ministan ya bada cikakkiyar hujja sannan ko gidan zai iya komawa gare sa,idan kuma bahaka ba,toh gwamnatin tarayya zata karbe gidan ya zama mallakin ta.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Shafin Facebook
Shafin Twitter
Shafin Instagram
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: [email protected]

Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa


Shiga Mujallarmu YouTube channel kayi subscribe domin kallon bidiyo da muka tanadar maka don nishadi da ilimantarwa
Updated: 2018-02-07 — 12:32 pm

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme