MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

WATA SABUWA: RIGIMA TA SHIGA TSAKANIN SAUDIYYA DA KASAR CANADA-Karanta Kaji Dalili

             Ko Miye Dalilin Rigima Tsakanin Kasar Saudiyya Da Canada-Karanta Kaji

Kasar Saudiyya ta kori Jakadan Kanada daga kasarta kamfanin dillancin labaran kasar ya ce shi ma jakadan Saudiyya a birnin Ottawa na Canada an bukaci ya koma gida

An yanke huldar kasuwanci tsakanij kasashen biyu Me ya hado Saudiyya da kasar Canada rigima? Kasashen Turawa kan yi kokarin gaya wa kasar Saudiyya gaskiya, wadda ke tsarin mmulukiyya ba dimokuradiyya ba,ana yawan kame masu fadin albarkacin bakinsu a kasar kuma ana hana su damar kare kansu.

Kasar Saudiyya ta kama wasu masu rajin kare hakkokin mata, duk da kasar Saudiyyar na tauye wa mata hakkoki karkashin tsarin shari’ar Islama.

Kasar Canada mai makwabtaka da AMurka, ta soki kasar Saudiyya wajen kama wasu mata wadanda suka bada gudummawar wayar wa da mata kai har suka sami ‘yancin yin tukin mota a kasar a bana.

Saudiyya taji haushin kushen, inda ta kira lammarin da cewa kutse ne cikin lamarin kasar ta, inda ta kori jakadan kasar ta Canada, kuma ta kira nata data jakadan daga kasar da ya dawo gida har warware. ta kuma dakatar da harkar kasuwanci tsakanin kasashen biyu.

Danna nan idan kana neman BIDIYON HAUSA masu ilimantar wa da NIshadantarwa musamman na Zamantakewa tsaknin Ma'aurata:


Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa

Updated: 2018-08-06 — 6:30 pm

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme