MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

WATA SABUWA: MUKADDASHIN SHUGABAN KASA OSINBAJO YA TSIGE SHUGABAN HUKUMAR DSS LAWAN DAURA-Karanta Kaji Dalili

       Yanzu yanzu: Mukaddashin shugaban kasa ya tsige shugaban hukumar DSS

Rahoton da muke samu daga fadar gwamnati shine mukaddashin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya tsige shugaban hukumar tsaro ta sirri, wato DSS, Malam Lawal Daura daga mukaminsa biyo bayan farmakin da jami’an hukumar suka kai majalisar dokokin Najeriya da safiyar ranar Talata 7 ga watan Agusta.

Dandalin Mujallarmu ta ruwaito Kakakin mataimakin shugaban kasa Osinbajo, Laolu Akande ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, 7 ga watan Agusta.

Haka zalika hadimin shugaban kasa Buhari akan harkokin sadarwar zamani, Bashir Ahmad ya tabbatar da fatattakar Lawal Daura daga aiki. Bugu da kari, Farfesa Osinbajo ya umarci Lawal Daura ya mika ragamar tafiyar da hukumar ga jami’I mafi girma a hukumar, har sai baba ta ji.

Lawal Daura Idan za’a tuna, da safiyar yau ne jami’an DSS suka tare kofar shiga majalisar dokokin Najeriya, inda suka hana wasu Sanatocin jam’iyyar PDP shiga farfajiyar majalisar, duk da cewa majalisar na hutu, har sai watan Satumba za’a bude ta.

Sai daga daga bisani bayan yan majalisun sun matsa, jami’an sun bude musu hanya, wannan tataburza da aka sha tsakanin Sanatoci da Jami’an DSS ya biyo bayan jita jitan da ake yadawa na cewa wai Sanatocin APC zasu tsige shugaban majalisar dattawa, Sanata Bukola Saraki.

Danna nan idan kana neman BIDIYON HAUSA masu ilimantar wa da NIshadantarwa musamman na Zamantakewa tsaknin Ma'aurata:


Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa

Updated: 2018-08-07 — 5:49 pm

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme