MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

WATA SABUWA: MAJALISAR DATTAWA TA NADA SABON KARAMIN AKAWU NA RIKON KWARYA-Karanta Kaji

Majalisar Dattawa Ta Amince Da Nadin Patrick Giwa Matsayin Sabon Karamin Akawu Na Rikon Kwarya

An nada Giwa ne bayan ritayar tsohon karamin akawun majalisar a ranar Lahadi, 25 ga watan Nuwamba ya fara aiki a ranar Litinin, 26 ga watan Nuwamba A yau, Litinin, 3 ga wata ne majalisar tarayya ta amince da nadin Patrick A Giwa a matsayin mukaddashin karamin akawun majalisar.

Kafin nadinsa, Giwa ya kasance mataimaki ga karamin akawun majalisar da ya yi ritaya daga aiki a ranar Lahadi, 25 ga watan Nuwamba. Sanarwar nadin Giwa na kunshe ne cikin wata sanarwa da Alhaji M A Sani-Omolari, babban akawun majalisar, ya aike ga dukkan ma su rike da mukami a majalisar. Majalisar wakilai Sanarwar ta ce,

“majalisar wakilai ta amince da nadin Patrick A Giwa a matsayin karamin akawun majalisar wakilai na rikon kwarya, nadin ya fara aiki ne daga ranar 26 ga watan Nuwamba.”

Danna nan idan kana neman BIDIYON HAUSA masu ilimantar wa da NIshadantarwa musamman na Zamantakewa tsaknin Ma'aurata:


Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa

Updated: 2018-12-04 — 1:08 am

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme